Buhari Ya Roƙi Yan Najeriya Su Yafe Masa Abin Da Ya Musu Ba Dai-Dai Ba

Buhari Ya Roƙi Yan Najeriya Su Yafe Masa Abin Da Ya Musu Ba Dai-Dai Ba

  • Shugaban Kasa Muhammadu ya nemi afuwar yan Najeriya a yayin da ya ke daf da sauka daga mulki a karshen wa'adinsa na biyu
  • Buhari ya bukaci duk wani wanda ya yi wa ba dai-dai ba yayin gudanar da ayyukansa ya yafe masa, ya kuma yi godiya bisa hakuri da aka yi da shi
  • Shugaba Buhari, wanda ya ce yana shirin komawa can garinsu Daura ya tare bayan ya sauka, ya yi wannan rokon ne a ranar Juma'a yayin tarbar al'umma Abuja da suka kawo masa ziyarar sallah

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga yan Najeriya da ta yi wu ya yi wa ba dai-dai ba yayin gudanar da ayyukansa su yafe masa, Daily Trust ta rahoto.

Ya yi wannan rokon ne a yayin ziyarar sallah ta tara kuma ta karshe a matsayinsa na shugaban kasa da mutanen babban birnin tarayya Abuja suka kai masa karkashin jagorancin Ministan Abuja, Mohammed Bello, a dakin taro na Banquet a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Kara karanta wannan

“Na Matsu Na Koma Mahaifata Daura”: Inji Buhari Yayin da Ya Yi Bikin Sallah Na Karshe a Aso-Rock

Shugaba Buhari
Buhari Ya Roƙi Yan Najeriya Su Yafe Masa Abin Da Ya Musu Ba Dai-Dai Ba. Hoto: @NigeriaGov
Asali: Twitter

Ina godiya bisa hakuri da aka yi da ni na shekara takwas, Buhari

Shugaban kasar ya kuma mika godiyarsa ga yan Najeriya bisa hakuri da su da suka yi na tsawon shekaru bakwai da suka shude.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya fada wa bakinsa cewa:

"Na gode bisa hakuri da ni ... Ina yi wa Allah godiya bisa baiwar da ya min na zama gwamna, minista da shugaban mulkin soja yanzu kuma shugaban kasa sau biyu.
"Na kosa in tafi gida... Da gangan na shirya yadda zan yi nisa da ku. Na samu abin da na nema kuma zan koma garin mu Daura in yi ritaya."

Ina son yin nesa da Abuja bayan na sauka daga mulki, Buhari

Shugaba Buhari, wanda ya kambana dimokradiyya a matsayin tsarin gwamnati mafi dacewa, ya ce ba domin shi ba, da bai zama shugaban kasa ba bayan yin shugabancin kasa na mulkin soja kuma bisa la'akari da bangaren da ya fito.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Hana Buhari Tsoma Baki a Tirka-Tirkar Binani da Fintiri – Gwamnatin Tarayya

Ya tunatar da mutanen da suka kawo masa ziyarar cewa ya fito ne daga wani lungu na Najeriya, Daura a Jihar Katsina, wacce tsakaninta da Jamhuriyar Nijar kilomita takwas ne kawai.

Masu Addinin Gargajiya A Najeriya Na Son A Tsayar Musu Ranar 20 Watan Agusta A Matsayin Hutu

A wani rahoton kun ji cewa yan kungiyar mabiya addinin gargajiya na Iseselagba ta kasa sun gabatar da bukatarsu ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya na neman a ware musu ranar hutu kamar sauran yan kasa mabiya wasu addinan.

Kakakin Kungiyar, Lawal, ya ce kuma ce bai dace a rika mantawa da mabiya addinan gargajiyan wurin rabon mukamai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164