Yan Sanda Sun Cafke Wani Sanannen Hatsabibin Mai Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Yan Sanda Sun Cafke Wani Sanannen Hatsabibin Mai Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

  • Wani shahararren da garkuwa da mutane da ake kira Chiyawa ya shiga hannun yan sanda a Jihar Nasarawa
  • Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta ce Chiyawa ya dade cikin jerin wanda ta ke nema ruwa a jallo
  • Hukumar ta kuma yi baja kolin karin wasu masu laifin wanda biyu daga ciki ke da alaka da garkuwa da mutane

Nasarawa - Rundunar yan sandan Jihar Nasarawa ta ce ta yi nasarar dakume wani shahararren mai garkuwa da mutane, Shuaibu Mohammed, da aka fi sani da Chiyawa, wanda ya aikata laifukan garkuwa da dama a jihar.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, shi ya bayyana haka a hedikwatar hukumar da ke Lafia ranar Alhamis yayin da ake baje kolin masu laifi da aka kama a kananan hukumomin jihar 13, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya dauki tsattsauran mataki kan jami'in INEC da ya dagula zaben Adamawa

Jihar Nasarawa
Yan sanda sun kama masu garkuwa a Nasarawa. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Ya yaba wa yan sandan da ke sashen dakile masu garkuwa da mutane, karkashin jagorancin SP Lapshak Lenka, bisa aiki tukuru don tabbatar da nasarar kama dan garkuwar, rahoton This Day.

Da yake jaddada aniyar hukumar na kawar da laifuka a kananan hukumomin jihar 13, Nansel ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kama duk wanda zai zama barazana ga zaman lafiyar jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Ranar 19/4/2023 da misalin 5:00 na yamma, bisa wani tsegumi, jami'an hana ayyukan garkuwa na hukumar yan sanda sun kama wani dan garkuwa Shuaibu Mohammed da aka fi sani da Chiyawa 'Namiji' daga Kadarko, da ke Giza.
"Wanda ake zargin da bincike ya tabbatar da jagoran wata shaharriyar kungiyar garkuwa ne da suka addabi Dadere, Maraba Akunza, Lafia, Agyaragu, Kadarko da kewaye, ya kasance cikin jerin wanda yan sanda ke nema bisa zargin ayyukan garkuwa kuma ya sha gujewa kame kafin ya shiga hannu."

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wasu Muggan Mutane Sama da 20 Ɗauke da Makamai Ana Dab da Sallah a Arewa

An yi holen wasu da ake zargi da laifuka

Baya da haka, hukumar ta kuma yi baja kolin wasu masu laifi biyu da ke da hannu a abin da ya shafi garkuwa da fashi da makami a karamar hukumar Lafia da ke Jihar.

Da yake zantawa kan batun, mai magana da yawun yan sandan ya ce:

"Ba da jimawa ba, bayan samun bayanan sirri, mun yi nasarar kama wasu da suka dade a jerin wanda muke nema bisa zargin garkuwa da mutane, Adamu Gagare Sule mai shekara 25 da Umar Idris dan shekara 20, a kauyen Kiguna, da ke Lafia ta Gabas.
"Da ake tuhumarsu, wanda ake zargin sun amsa garkuwa da mutane hudu tare da kai su maboya a daji da ke karamar hukumar Qua'anpan ta Jihar Plateau tare siyawa mutanen abinci kafin su yi nasarar tserewa.
"Sannan, wanda ake zargin sun amsa aikata laifukan garkuwa da fashi da makami a Lafia ta gabas, Awe da Jenkwe da ke karamar hukumar Obi."

Kara karanta wannan

Abin da Ya Hana Buhari Tsoma Baki a Tirka-Tirkar Binani da Fintiri – Gwamnatin Tarayya

Da yake jan kunne ga duk masu sha'awar aikata laifi da su bar Nasarawa ba tare da bata lokaci ba, DSP Nansel ya ce kwamishinan yan sanda, CP Maiyaki Baba, ya bada umarnin a kai wadanda ake zargi zuwa kotu idan an kammala bincike a sashen binciken manyan laifuka na hukumar da ke Lafia.

An Kama Mai Garkuwa Yana Karbar Kudin Fansa A Plateau

A wani rahoton, yan sanda a jihar Plateau sun kama wani da ake zargin mai satar mutane ne yayin da ya ke karbar kudin fansa naira miliyan 3.

Bartholomew Onyeka, kwamishinan yan sandan jihar Benue ya tabbatar da kamen yayin da ya ke zantawa da yan jarida a Jos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164