Jam’iyyar APC Ta Ci Gaba da Zama Mafi Rinjaye a Majalisar Wakilai Tare da Kujeru 134

Jam’iyyar APC Ta Ci Gaba da Zama Mafi Rinjaye a Majalisar Wakilai Tare da Kujeru 134

  • Majalisar wakilai ta kasa za ta ci gaba da zama karkashin rinjayen jam’iyyar APC mai mulki bayan kammala zaben cike gurbi
  • An bayyana adadin kujerun da APC da sauran jam’iyyun siyasa suka samu a zaben da aka karasa a ranar 15 ga watan Afrilu
  • A bangare guda, majalisar dattawa ta kasa ma za ta zama karkashin rinjayen jam’iyyar APC, ita tafi kowacce jam’iyya yawan sanatoci

Najeriya - Jam’iyyar APC ta ci gaba da zama mafi rinjaye a majalisar wakilai ta Najeriya, inda ta samu mafi yawan kujerun majalisa a zaben bana da aka kammala.

Har yanzu, ana ci gaba da sanar da sakamakon zaben majalisar wakilai ta kasa da ake karasawa a zaben cike gurbin da aka gudanar ranar Asabar 15 ga watan Afrilu.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta jagoranci gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Faburairu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa: APC ta lashe kujeru 59, an fadi yawan na PDP, NNPP, LP da SDP

Majalisa ta 10 za ta cika da 'yan APC
Majalisar wakilai ta Najeriya | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Sai dai, an samu tsaiko a lokacin zaben, wanda hakan ya sanya aka dage shi a wasu yankuna tare da sanar da ranar zaben cike gurbi a matsayin 15 ga Afrilu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda zaben 25 ya kasance da sakamakonsa

Bayan zaben 25 ga watan Faburairu, shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya sanar da cewa, an kammala zaben majalisar kasa na kujeru 423 cikin 469, kuma an sanar da sakamakonsu.

A cewarsa, daga ciki, an sanar da 325 na majalisar wakilai daga 360, yayin da sauran kuma suka kasance na sanatoci a kasar, Tribune Online ta tattaro.

A cewar Farfesa Yakubu, a majalisar wakilai ta kasa, APC ta samu kujeru 162 yayin da jam’iyyar PDP kuma ta samu kujeru 102.

Ya kara da cewa, jam’iyyar Labour da NNPP ta su Kwankwaso sun samu kujeru 34 da 18 bi da bi, APGA ta samu hudu, sai kuma ADC da SDP masu kujeru biyu kowanne da kuma YPP mai kujera daya tak.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Gagarumin Gargadi Ga INEC Kan Zaben Adamawa, Ya Nemi a Kama Jami'an Zabe

Zaben cike gurbi da aka gudanar da sakamakonsa

A tun farko, INEC ta ce za a gudanar zaben cike girbin ne a mazabu 46 na kasar nan don cike zaben ‘yan majalisun wakilai na tarayya.

Ya zuwa jiya da ake tattara sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata, APC ta samu kujeru 174, PDP 107, Labour 35, NNPP 19 da kuma APGA mai guda 5.

Wannan na nufin, APC ce za ta ci gaba da zama mafi rinjaye a majalisar wakilai ta kasa a majalisa ta 10 da za a rantsar a watan Yuni.

Haka batun yake ga majalisar dattawa, jam’iyyar APC ce ta fi yawan kujerun sanata a zaben da aka kammala kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.