Yan Daba Sun Sace Akwati Da Kayan Zabe Yayin Zaben Cike Gurbi A Katsina, Wakilin PDP

Yan Daba Sun Sace Akwati Da Kayan Zabe Yayin Zaben Cike Gurbi A Katsina, Wakilin PDP

  • Wasu matasa da ake zargin yan daba ne sun yi awon gaba da akwatin zabe da sauran kayan aikin zabe a mazabar Kankara da ke Katsina
  • Nurudeen Sani, wakilin jam'iyyar PDP da ke kula da mazabar Kankara ne ya yi wannan zargin yana mai cewa jami'an tsaro suna kallo aka aikata hakan
  • Sani ya kuma ce su a wurinsu suna ba wa hukumar zabe shawara ta mika shaidar nasara ga dan takarar PDP, Lawal Audu, don shi ke kan gaba kafin a tarwatsa zaben

Jihar Katsina - Wasu da ake zargin yan daba ne sun kawo cikas yayin gudanar da zaben cike gurbi da aka yi a gundumomi tara na Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina, Channels TV ta rahoto.

Hukumar Zabe INEC na gudanar da zabukan cike gurbin ne na kujeru uku a Majalisar Dokokin Jihar Katsina da suka kunshi Kankara, Kurfi da Kankia.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Bayan dogon kai ruwa rana, Ado Doguwa ya lallasa dan tsagin Kwankwaso

Zaben Katsina.
Wasu da ake zargin yan daba ne sun tsere da kayayyakin zabe a yayin zaben cike gurbi na yan majalisu a Katsina. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya faru

Wakilin jam'iyyar PDP da ke kula da mazabar Kankara, Nurudeen Sani, ya yi wannan zargin a ranar Asabar, yana mai cewa abin takaici ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar wakilin jam'iyyar, an fara zaben cikin lumana, amma daga bisani abubuwa suka rikice bayan wasu bakin fuskoki da suka yi ikirarin su masu ruwa da tsaki ne na jam'iyyar APC, da wakilai da shugaban karamar hukuma da yan sandan su.

Ya yi ikirarin cewa wasu da ake zargin yan daba ne sun kwace kayayyakin zabe a gaban yan sanda da sauran jami'an tsaro hakan yasa suka tsorata wakilan PDP.

A ba wa PDP nasara domin dan takarar mu ke kan gaba, Wakilin PDP

Amma, ya yi kira ga hukumar zaben ta mika satifiket din nasara ga dan takarar PDP, Lawal Audu, a matsayin wanda ya lashe zaben domin shi ke kan gaba da kuri'u 6,104 cikin 11,000 da aka kada a zaben na baya-bayan.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Jam'iyyar APC ta sake cin kujerar sanata a wata mazabar Yobe

Ya kara da cewa:

"Shugaban karamar hukumar Kankara, Anas Isah, ya riga ya tattaro yan daba don su kawo cikas ga zaben. Iya saninmu, ba a yi zabe a dukkan akwatuna a yankin nan ba.
"Wawar-Kaza, Kuka-Sheka, Burdugau, Pauwa A, Pauwa B, Danmarago, da Dan Maidaki na cikin wasu gundumomin da abin ya shafa.
"An hada kan shugabannin kananan hukumomin uku su kawo cikas ga zaben."

A hirar da aka yi da shugaban karamar hukumar Kankara, Hon. Anas Isah, ya ce yana da kwarin gwiwa sosai cewa APC za ta lashe zabukan.

Ya kuma ce ya gamsu da yadda mutane suka fito kwansu da kwarkwata.

Ba ka riga ka zama gwamnan Kano ba, Ganduje ya fada wa Abba

A wani rahoton gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Ganduje ya gargadi Abba K. Yusuf, gwamna mai jiran gado ya dena katsalandan a mulkin jihar.

Gandujen ya ankarar da Abba cewa shi ne gwamna har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023 don haka ba shi da hurumin bada umurni a hukumance.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Majalisa Na Jam'iyyar Labour Ya Dauki Hayar Makasa Sun Kashe Abokin Hamayarsa Na PDP A Ebonyi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164