Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kashe Mutane Tara a Jihar Yobe
- Mayakan Boko Haram sun kai mummunan hari kan al'ummar Buni Gari da ke jihar Yobe
- Yan ta'addan sun murkushe mutane tara yayin da suka je neman wani dan uwansu a cikin jeji
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar al'amarin
Yobe - Wasu da ake zaton mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram ne sun kai sabon hari a jihar Yobe, inda suka kashe akalla mutum tara.
Channels TV ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu a Buni Gari, karamar hukumar Gujba da ke jihar.
Mazauna garin Buni Gari, Baba Ibrahim da Iliya Maina sun sanar da Channels TV cewa al'ummar yankin sun shiga tashin hankali ne lokacin da wani mutum mai suna Shettima Dawi ya tafi neman itattuwa a yan kilomita kadan da garin amma bai dawo ba.
Lamarin ya sa yan uwanda da makwabta haduwa don gano inda yake a cikin jeji, kawai sai mayakan Boko Haram suka farmake su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mazauna yankin sun ce:
"Wasu da ake zaton yan ta'adda ne sun kashe mutane 10 bayan sun je neman dan uwansu (Shettima Dawi) wanda ya bar gida a jiya (Alhamis) don tsintan itatuwa a yan kilomita kadan daga Buni Gari amma bai dawo gida ba.
"Daga cikin dukkan mutane 10 da suka je jejin don neman Shettima, mutum daya ne kawai ya tsira da raunuka kuma yana samun kulawar likitoci, an kashe sauran mutanen harda Shettima Dawi."
Rundunar yan sanda ta tabbatar da harin
Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da harin.
DSP Abdulkarim, ya ce sabanin abun da rahotanni suka kawo, mutane tara yan ta'addan suka kashe.
Duk kokarin jin ta bakin Daraktan hulda na jama';a na rundunar sojin Operation Hadin Kai, Kyaftin Kennedy Anyawu ya ci tura don wayarsa bata zuwa.
An tattaro cewa dakarun soji da yan banga sun kwashi gawarwakin mutanen da abun ya ritsa da su daga ramin yan ta'addan.
Buni Gari, wanda ke a yankin dajin Sambisa, ya kasance mahaifar Gwamna Mai Mala Buni.
Ku tuna cewa gaba daya yankin Gujba ya kasance karkashin ikon mayakan Boko Haram tsakanin 2012 da 2014.
Yan fashi sun farmaki kasuwar Ogun, sun kashe mutum daya
A wani labari na daban, wasu mutane da ake zaton yan fashi da makami ne sun farmaki kasuwar wayoyi na Abeokuta, jihar Ogun inda suka kashe mutum daya.
Asali: Legit.ng