Ku Sanya Najeriya a Addu’o’i: Sarkin Musulmi Ga Duk Wani Musulmin Najeriya a 10 Na Karshen Ramadana
- Rahoto ya bayyana kiran da Sarkin Musulmi ya yiwa ‘yan Najeriya yayin da aka shiga 10 na karshen watan Ramadana
- Shugaban ya bayyana cewa, akwai bukatar al’umma su mayar da hankali ya yiwa kasa addu’o’in ci gaba da fatan alheri
- A baya kunji yadda kasar Kuwait ta hana limamai amfani da wayoyin hannu wajen yin karatun sallah a cikin watan Ramadana
Jihar Sokoto - Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ta bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da kwanaki 10 na karshen watan Ramadan don yiwa kasa addu’ar zaman lafiya.
A cewar sarkin Musulmi, wannan dama ce ga Musulman kasar don yiwa kasar add’uar ci gaba, tsaro da kuma kwanciyar hankali, rahoton jaridar Daily Trust.
A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Talata ta hannun babban sakatarenta, Dr Khalid Abubakar Aliyu, JNI ta yi kira ga Musulman Najeriya mazauna gida da wadanda suka tafi Umrah da su kara zage damtse da addu’o’in neman tsari.
Hakazalika, kungiyar ta ce kowa ya mai da hankali ga yiwa gwamnatin kasar addu’o’in kariya da kuma gamuwa da alheri a gwamntin Tinubu da ke tafe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Goman karshe na Ramadana suna daraja
A bangare guda, JNI ta tunatar da Musulmi cewa kwanaki 10 na karshe sukan zo da mafi falalar darare daga cikinsu, wanda a ciki ne ake gamo da daren lailatul kadari, wanda ya fi darare dubu.
JNI ta kara kwadaitar da musulmi da su kara himma wajen yawaita ayyukan alheri da kuma ambaton Allah, da neman gafararSa, yin tilawar Alkur'ani, halartar tafsiri, da nisantar duk wani aiki ko yasasshiyar magana, rahoton 21st Century Chronicle.
Ba wannan ne karon farko da fadar Sarkin Musulmi ke tura sakon shawari ga ‘yan Najeriya ba, musamman a yanayi irin wannan mai bukatar mayar da hankali.
An haramtawa limamai amfani da wayar hannu a lokacin sallolin dare
A wani labarin, kun ji yadda kasar Kuwait ta bayyana haramtawa limamai amfani da wayoyin hannu wajen karatun sallah.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da al’umma ke ci gaba da karbar manhajojin wayoyin hannu na Al-kur’ani mai girma.
Kasar ta bayyana cewa, yin tilawa a sallar ne zai taimakawa mutane wajen kiyaye kaifin hadda da kuma shajja’a masu sha’awar karatun littafin mai tsarki.
Asali: Legit.ng