Yanzu Yanzu: An Tsare Peter Obi a Filin Jirgin Sama Na Kasar Ingila
- Jami'an hukumar kula da shige da fice na Ingila sun kwamushe dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi
- Hukumomi a Ingila sun tsare Obi ne lokadin da ya isa filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan don bikin Easter
- Kakakin kungiyar kamfen din Obi-Datti, iran Onifade, ya ce an yi wa ubangidan nasu tambayoyi bayan wani ya yi basaja da sunansa
An tsare dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi a Landan, kasar Birtaniya inda ya je bikin Easter, kakakin kungiyar kamfen din Obi-Datti, iran Onifade, ya bayyana.
A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu, Onifade ya kuma bayyana cewa jami'an hukumar kula da shige da fice na Landan sun ci zarafin Obi sannan suka tsare shi, jaridar Daily Trust ta rahoto.
A cewarsa, Obi ya isa filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan daga Najeriya a ranar Juma'a, 7 ga watan Afrilu sannan ya bi layi don cike ka'idojin filin jirgin saman lokacin da jami'an suka kwamushe shi sannan suka nemi ya gefe.
Onifade ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An yi masa tambayoyi na tsawon lokaci sannan hakan bakon lamari ne ga mutumin da ya shafe tsawon fiye da shekaru 10 a wannan kasar.
"Babban illar da ke tattare da laifin shine cewa mai basajan zai iya aikata irin wannan manyan laifuka da sauran ayyukan rashin gaskiya da sunan Obi."
Ya kuma tuna cewa jami'an hukumar kula da shige da ficen sun cika da mamaki da martanin mutane inda hakan ya tilasta masu fadama wadanda ke wajen cewa Obi na amsa tambayoyi ne, rahoton Channels TV ta rahoto.
Tun bayan zaben shugaban kasa Obi ke fuskantar hare-hare, Onigade
Onigade ya kuma tuna cewa Obi na ta fuskantar hare-hare iri-iri tun bayan zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu wanda ya zo na uku a cikinta.
Ya kuma ce masu lura da zaben da dama ciki harda yan kungiyoyin kasa da kasa da magoya bayansa da wasu da dama sun yarda cewa shine ya lashe zaben amma aka yi magudi.
Obi na da tambayoyi da zai amsa kan sautin muryarsa da aka bankado, FG
A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta a kan sautin muryar Peter Obi da malamin addini, Bishop David Oyedapo da aka bankado.
Ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed ya bukaci Obi ya yi karin haske kan abun da yake nufi da sautin muryar da aka bankado na bogi ne.
Asali: Legit.ng