Suna Dab Da Barin Mulki, Hadimin Shugaba Buhari Ya Yi Wa Shahararren Malamin Addini Kaca-Kaca

Suna Dab Da Barin Mulki, Hadimin Shugaba Buhari Ya Yi Wa Shahararren Malamin Addini Kaca-Kaca

  • Hadimin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi wa Bishop Matthew Kukah, wankin babban bargo
  • Femi Adesina ya ce malamin addini ya aje rigar malinta kawai ya kama siya ba ƙaƙƙautawa
  • Ya zargi malamin da sanya siyasa idan zai yi magana kan abubuwan da suke faruwa a ƙasar nan

Abuja- Hadimin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya cacccaki sanannen faston nan na cocin katolika, Bishop Matthew Kukah, kan sukar nasarorin da gwamnatin mai gidan sa ta samu.

A cewar Adesina, akwai siyasa a cikin ra'ayoyin da Kukah yake bayyana wa kan siyasar ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa ya cire rigar malinta kawai ya koma siyasa gadan-gadan, rahoton Tribune ya tabbatar.

Adesina ya caccaki Bishop Kukah
Hadimin shugaba Buhari da Bishop Kukah Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

Kalaman Adesina na zuwa ne a matsayin martani kan tambayar da Kukah ya aike wa shugaba Buhari, cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Namijin Kokarin da Buhari Ya Yi Na Dawo da Zaman Lafiya a Najeriya

A cikin sanarwar, Kukah ya tambayi shugaba Buhari ko ya cika alƙawarin da yi wa ƴan Najeriya na magance matsalar tsaro da cin hanci da rashawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake mayar da martani a nasa jawabin, Adesina ya bayyana cewa shugaba Buhari ya samar da cigaba sosai a fannin magance matsalar tsaro.

A kalamansa:

"Wani yace zai fi kyau idan Kukah zai aje rigar malinta gefe ɗaya sannan ya koma cikakken ɗan siyasa."
“Kukah ya cika siyasa a lamuran sa. Mutum ne wanda muke mutuntawa saboda baiwar da yake da ita."
"Amma ra'ayoyin sa yana sanya siyasa a ciki. Yayi maganar siyar da jiragen shugaban ƙasa. Dama an taɓa alƙawar ta hakan ne?"

Ya cigaba da cewa:

“A shekarar 2015, akwai tulin alƙawarurruka da akayi wanda ko shi kan shi ɗan takarar baya da masaniya akan su."

Kara karanta wannan

An Kunno Wa Fitaccen Ministan Buhari Wuta, Ana Neman Gwamnatin Tarayya Ta Cafke Shi

“Tambayar itace, shin yanzu a yadda muke kan matsalar tsaro haka muke a shekarar 2015? Har yanzu akwai sauran rina a kaba amma shin a inda muka baro baya muke?"
“Idan Kukah zai gayawa kansa gaskiya kuma ya mutunta kiran da ake masa na malami, ya san cewa ƙasar nan ba a haka take ba yanzu kan matsalar tsaro idan aka kwatanta da shekarar 2015."

Yan Kwamiti Sun Fusata Sun Dakatar Da Shugaban Jam'iyyar APC

A wani rahoton kuma, kun ji yadda ƴan kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC a wata mazaɓa a jihar Ondo suka dakatar da shugaban jam'iyyar na mazaɓar.

Ƴan kwamitin sun bayyana rashin sanin makamar aiki a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya suka dakatar sa shugaban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng