Wadanda Suka Sace Tsohon Mataimakin Gwamna Sun Bukaci Fansar N70m
- Daga karshe yan bindigan da suka sace tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Farfes Onje Gye-Wado sun nemi iyalansa su biya naira miliyan 70 don fansarsa
- Wata majiya da ke sanya ido kan lamarin ta rahoto cea iyalan tsohon mataimakin gwamnan sun roki masu garkuwan su yi hakuri su karbi naira miliyan biyu su sako shi
- Iyalan sun koka cewa ba su da inda za su tafi su nemo wani kudin saboda hutun bukukuwan Good Friday da Easter da gwamnatin tarayya ta bada daga ranar Juma'a zuwa Litinin
Jihar Nasarawa - Wadanda suka sace tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye-Wado, sun bukaci a ba su naira miliyan 70 matsayin kudin fansarsa, The Punch ta rahoto.
Wani majiya wacce ke bibiyan lamarin ta sanar da jaridar Daily Trust a Lafia, babban birnin jihar, cewa daga karshe wadanda suka sace shi sun tuntubi iyalansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tunda farko wakilin Daily Trust ya rahoto cewa an sace Onje Gye-Wado ne a safiyar ranar Juma'a a kauyen Gwagi da ke karamar hukumar Wamba na jihar ta Nasarawa.
Majiyar ta kara da cewa iyalan suna ta rokon masu garkuwan su yi hakuri su karbi naira miliyan 2 a maimakon miliyan 70 da suka nema da farko saboda rashin tsabar kudi.
Ya ce:
"Wadanda suka sace shi sun riga sun tuntubi iyalan Farfesan kuma sun nemi a biya su naira miliyan 70, amma muna rokonsu su karba naira miliyan 2 saboda ba za mu iya samun fiye da hakan ba duba da hutun bikin Easter da Gwamnatin Tarayya ta bada."
"Daga yau Juma'a, har zuwa ranar Litinin, hutu ne, babu inda za mu samo kudi kuma muna son a dawo mana da shi (Prof) din da ransa."
Asiru Ya Tonu: An Cafke Wani Mai Garkuwa Da Mutane Lokacin Yana Karbar Fansar Naira Miliyan 3 Daga Hannun Iyayen Wanda Ya Sace
A wani rahoton, kun ji cewa jami'an yan sanda a jihar Filato sun cafke wani mutum da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a yayin da ya ke kokarin karbar kudin fansa har N3m daga hannun mahaifin wani da ya sace.
Bartholomew Onyeka, kwamishinan rundunar yan sandan jihar Benue ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a yayin da ya ke bayyana nasarorin da hukumar ta samu.
Asali: Legit.ng