Yajin Aiki: Duk Da Shugaba Buhari Ya Sako Kudi, ASUU Tace Akwai Sauran Rina a Kaba

Yajin Aiki: Duk Da Shugaba Buhari Ya Sako Kudi, ASUU Tace Akwai Sauran Rina a Kaba

  • Ƙungiyar Malaman Jami'a ta ƙasa (ASUU) tace gwamnatin tarayya bata cika mata mafiya yawan buƙatun ta ba
  • Shugaban ƙungiyar na ƙasa ya ce Gwamnatin Tarayya bata neme su ba tun bayan janye yajin aiki
  • Shugaban ya kuma yaba da umurnin gwamnatin tarayya na a fitar da maƙudan kuɗi domin makarantun gaba da sakandiren gwamnati

Abuja- Shugaban ƙungiyar malaman jami'a ta ƙasa (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodoke, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya har yanzu bata biya mafi yawa daga cikin buƙatun malaman ba tun lokacin da suka janye yajin aikin su a shekarar 2022.

Osodeke wanda ya yi magana a yayin wata tattaunawa da gidan Talbijin na Channels TV, a daren ranar Alhamis, ya bayyana cewa bayan ƙungiyar ta janye yajin aikin gwamnatin tarayya bata ƙara neman su ko sau ɗaya ba, rahoton Punch

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Daba Sun Kutsa Kai Cikin Sakatariyar Jam'iyya Ta Ƙasa a Abuja

Shugaban ASUU
Yajin Aiki: Duk Da Shugaba Buhari Ya Sako Kudi, ASUU Tace Akwai Sauran Rina a Kaba Hoto: Punch
Asali: Facebook

A cewar rahoton Leadership, hakan na zuwa ne dai bayan a kwanan nan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince da a fitar da N320,345,040,835 domin farfaɗo da makarantun gaba da sakandiren gwamnati a ƙasar nan.

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Su a wajen wannan gwamnatin da an janye yajin aiki shikenan an warware matsalar, abinda basu sani ba shine yajiɓ aiki alama ce ta matsala. Sun yi watsi da matsalar. Tun da muka janye yajin aikin bisa umurnin kotu, ko sau ɗaya ba a kora mu taro ba. Ko sisi ba a biya mu ba."
“Abin akwai takaici cewa basu ganin darajar ɓangaren ilmi a ƙasar nan."

Osodeke ya kuma ya yaba da amincewa a fitar da N320bn domin makarantun gaba da sakandiren gwamnati.

“Abu ne mai kyau, wannan yana daga cikin abinda mu kayi ta fafutuka akai a shekarar 1994, jajircewar mu ce, amma akwai abubuwan da muke buƙatar mu warware." Inji shi

Kara karanta wannan

Zababben Gwamnan APC Ya yi Kus-Kus Da Shugaba Buhari, Ya Ce Jiharsa Na Neman Dauki

A cewar gwamnatin tarayya kuɗin farfaɗo da makarantun na shekarae 2023, za su sanya kowacce jami'a ta samu N1,154,732,133.00, sannan kowacce kwalejin fasaha ta samu N699,344,867.00, yayin da kowacce kwalejin ilmi zata samu N800,862,602.

FG Na Daf Da Takaita Zirarewar Likitoci Fita Waje Aiki

A wani rahoton na daban kuma, gwamnatin tarayya na shirin dakatar da ficewa ƙasar nan da likitoci suke zuwa ƙasashen waje domin aiki.

Gwamnatin tarayya ta shirya kafa wata doka wacce zata hana yawan ficewa da likitocin ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng