Abun Tausayi: Mata da Miji da Ɗiyarsu Mace Sun Rasu a Gobara a Kaduna
- Lokaci ya yi, Wasu ma'aurata da ɗiyarsu sun rasa rayuwarsu sakamakon ibtila'in gobara a garin Kafanchan, jihar Kaduna
- Wani maƙocin gidan da lamarin ya faru ya ce sun fahimci wuta na ci a gidan da misalin karfe 11:00 na dare amma ƙofa taƙi buɗuwa
- Masarautar Jema'a da shugaban ƙaramar hukumar Jema'a sun kai ziyarar ta'aziyya ga 'yan uwan mamatan
Kaduna - Wasu ma'aurata da ɗiyarsu guda ɗaya sun ƙone har lahira yayin da gobara ta kama sunatsaka da bacci a garin Kafanchan, karamar hukumar Jema'a a jihar Kaduna.
Punch ta ce har kawo yanzu babu sahihin bayani kan abinda ya haddasa tashin gobarar amma mazauna garin sun ce sun fara ganin hayaƙi na fitowa daga gidan da karfe 11:00 na daren Talata.
Wani maƙocin ma'auratan, Maikano Abdullahi, wanda ya rasa kadarorinsa a ibtila'in wutar, ya ce duk wani yunkurin mutanen da suka kawo ɗauki na ceto iyalan gidan bai kai ga nasara ba.
A rahoton Vanguard, Abdullahi ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na tashi daga bacci lokacin da na jiyo muryar matata tana kururuwar neman taimako lokacin da Gobara ta mamaye ɗakin Zainab, wanda ke gaban ɗakinmu."
"Abinda ya auku ya yi muni, mun yi iya bakin kokari mu karya ƙofar domin ba zamu iya shiga ba saboda sun kulle ta."
"Bisa rashin sa'a ma'auratan, Abdurrahman Abdullahi, wanda muke kira Ɗanjummai, da matarsa, Zainab Nuhu, da ɗiyarsu Husna duk sun rasu a gobarar gabanin mu iya ɓalle kofar."
Ya ƙara da bayanin cewa mutanen da suka kawo ɗauki da wuri-wuri sun ji lokacin da matar gidan, Zainab, take neman a kawo musu ɗauki, ta ce ba abinda zasu iya yi saboda wutar ta kama ko ina.
Mamacin, Ɗanjummai, ma'aikaci ne a hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC).
Masarautar Jema'a ta hannun Madakin Jema'a kuma hakimin Fada, Alhaji Audi Muhammad da shugaban ƙaramar hukumar Jema'a, Yunana Barde, sun kai ziyarar ta'aziyya ga yan uwan mamatan.
Mahaifiyar Tsohon Minista a Najeriya Ta Mutu
A wani labarin kuma Tsohon Minista a Najeriya Ya Yi Babban Rashi, Mahaifiyarsa Ta Rigamu Gidan Gaskiya
Tsohon ministan sufurin jiragen sama a Najeriya, Osita Chidoka, ya tabbatar da mutuwar mahaifiyarsa mai shekara 75 a duniya.
A wata sanarwa da tsohon Ministan ya rattaɓa wa hannu a madadin iyalai, ya ce mahaifiyarsu ta cika cikin salama zagaye da iyalanta a gidanta da ke Legas.
Asali: Legit.ng