Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Kulle Majalisar Dokokin Jihar Plateau, Bayanai Sun Bayyana

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Kulle Majalisar Dokokin Jihar Plateau, Bayanai Sun Bayyana

  • Ƴan sanda sun dira majalisar dokokin jihar Plateau inda suna garƙame ƙofar shiga cikin ta
  • Bayanai sun nuna cewa ƴan sandan sun kulle majalisar a dalilin rikicin shugabancin majalisar da ya ɓarke
  • Majalisar dokokin jihar ta samu kanta cikin rikicin shugabanci tun bayan da kotu ta mayar ɗa tsigaggen shugabanta kan kujerar sa

Jihar Plateau- Ƴan sanda sun kulle harabar majalisar dokokin jihar Plateau. Hakan ya faru ne a dalilin rikicin shugabancin majalisar da ake ta tafkawa.

Tawagar ƴan sandan kwantar da tarzoma sun isa harabara majalisar dokokin jihar inda suka mamaye babbar ƙofar shiga cikin ta. Rahoton Daily Trust

Plateau
Yanzu-Yanzu: 'Yan Sanda Sun Kulle Majalisar Dokokin Jihar Plateau, Bayanai Sun Bayyana Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

Duk da cewa rundunar ƴan sandan jihar bata fitat da wanu bayani ba a hukumance kan wannan kullewar da ta yiwa majalisar, hakan baya rasa nasaba da rikicin da ya ɓarke tsakanin mambobin majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Shiga Cikin Jihar Kano, Sun Yi Garkuwa da Matar Wani Basarake da Ɗansa

Majalisar dokokin ta rabu gida biyu, inda wani ɓangare ke goyon bayan kakakin majalisar na yanzu Rt. Hon Yakubu Sanda, sannan ɗayan ɓangaren yake goyon bayan kakakin majalisar da kotu ta mayar kan muƙamin sa, Rt. Hon Ayuba Abok, wanda aka tsige a watan Oktoban 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata kotu ta mayar da Abok kan kujerar sa a ranar Litinin, sannan washe garin ranar Talata ya dira majalisar dokokin domin cigaba da jagorantar ta.

Sahara Reporters ta rahoto shugaban masu rinjaye na majalisar kuma shugaban kwamitin watsa labarai, Hon Nanlong Daniel, ya bayyana cewa:

"Bayan an tsige tsohon kakakin, majalisar ta bayyana kujerar sa a matsayin wacce ba kowa a kanta, wanda hakan ke nufin shi ba ɗan majalisar dokokin jihar bane sannan ba zai iya amfana da hukuncin kotun ba."
“Koma dai menene, majalisar bata da masaniya akan hukuncin kuma ba a aiko mana da shi ba. Muna jin labarin ne kawai a matsayin jita-jita. Duk lokacin da aka aiko mana da shi zamu yi magana akai."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗaliban Wata Makaranta a Jihar Kaduna

“Amma a yanzu bamu da masaniya kan hukuncin. Muna mutunta ɓangaren shari'a, sannan muna da zaɓin ɗaukaka ƙara duk lokacin da aka aiko mana da hukuncin. Amma a halin da ake ciki yanzu mu bamu san da wani hukunci ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng