Yanzu Yanzu: Buhari Ya Umurci Shugaban Hukumar NASENI Ya Sauka Daga Kujerarsa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke shugaban Hukumar NASENI, Farfesa Mohammed Sani Haruna daga kujerarsa
- Buhari ya tsawaita wa'adin Farfesa Haruna da shekaru biyu bisa kuskure bayan ya kammala wa'adinsa na shekaru biyar-biyar sau biyu
- An bukaci shugaban na Hukumar bunkasa kere-kere ta Najeriya da ya gaggauta mika mukaminsa ga babban jami'i na gaba a hukumar
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci shugaban Hukumar bunkasa kere-kere ta Najeriya (NASENI), Farfesa Mohammed Sani Haruna, da ya gaggauta yin murabus daga kujerarsa.
Shugaban kasar ya kuma bukace shi da ya mika shugabanci ga babban jami’i na gaba a hukumar, Daily Trust ta rahoto.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya fitar a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu.
Dalilin sauke shi daga kujerarsa
Ci gaban ya biyo bayan ganowa da aka yi cewa shugaban kasar ya yi masa karin wa'adin shekaru biyu bisa kuskure kasancewar ya riga ya kammala wa'adi biyu na shekaru biyar-biyar a hukumar, rahoton Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar ta ce:
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci shugaban hukumar bunkasa kere-kere ta Najeriya NASENI, Farfesa Mohammed Sani Haruna, da ya gaggauta mika kujerarsa ga babban jami'i na gaba a hukumar.
"Hakan ya biyo bayan janye karin wa'adin da shugaban kasa ya yi masa daga 2 ga watan Afrilun 2023 zuwa 2 ga watan Afrilun 2025 saboda EVC din ya kammala wa'adi biyu na shekaru biyar-biyar a hukumar.
"Shugaban kasar ya yaba da gudunmawar da Farfesa Haruna ya bayar wajen bunkasa bangaren kere-kere na tattalin arziki, kuma yana yi masa fatan samun nasara a ayyukansa na gaba.”
Buhari ba zai kara ko yini daya ba a kan mulki, Boss Mustapha
A wani labari na daban, babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya jaddada cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mika mulki ga gwamnati ta gaba a ranar 29 ga watan Mayu.
Mustapha ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ba zai kara ko da yini guda ba a kan mulki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ta tanada.
Asali: Legit.ng