Badakalar Batan N20bn Daga Asusun NNPCL, Gaskiya Ta Bayyana

Badakalar Batan N20bn Daga Asusun NNPCL, Gaskiya Ta Bayyana

  • Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya fito ya bayyana gaskiya kan ɓacewar N20bn daga asusun sa
  • Kamfanin yace zuƙi ta malle ce kawai ake ta ƴaɗawa akan sa amma babu ƙamshin gaskiya a ciki
  • Kamfanin ya kuma yi gargaɗi kan masu yaɗa wannan ƙarairayin akan sa da su shiga taitayin su

Abuja- Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), ya musanta rahotannin dake yawo cewa makuɗan kuɗaɗen da suma kai naira biliyan ashirin (N20bn) sun yi ɓatan dabo daga asusun ta.

Rahotannin dake yawo sun yi iƙirarin cewa kamfanin na NNPCL ya ƴan kwangilar bogi zunzurutun kuɗi har N20bn, zarfin da kamfanin yayi watsi da shi a matsayin ƙarya, inda yace baya mu'amala da ƴan kwangilar bogi. Rahoton The Cable

NNPCL
Badakalar Batan N20bn Daga Asusun NNPCL, Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Ait Live
Asali: UGC

Da yake mayar da martani kan rahotannin a ranar Litinin, kakakin kamfanin NNPCL, Garba Deen Muhammad, yace kamfanin ko kaɗan baya ƙulla alaƙa da ƴan kwangilolin bogi.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana, Dan Takarar Gwamnan APC Ya Tono Kulla-Kullar Da Ake Shirya Masa Don Hana Shi Zuwa Kotu

Yace hanyar da ake bi wajen ƙulla alaƙa da ƴan kwangila duk idan buƙatar hakan ta taso, hanya ce wacce aka amince da ita a faɗin duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"A dalilin hakan abin takaici ne akan koma wane irin dalili ne wannan kafar ta yanar gizo zata yi wannan mummunan zargin ba tare da abinda hakan zai janyo ba."
“Iƙirarin cewa N20bn tayi ɓatan dabo babu ƙamshin gaskiya ko kaɗan a cikin sa."

Muhammad ya kuma yi ƙarin haske kan zargin cewa NNPC na da hannu akan sace maƙudan kuɗin harajin da za a ba jihar Ogun. Rahoton Ait Live

"Ɓangare na biyo na wannan rahoton yana magane ne kan gwamnatin jihar Ogun na neman kuɗin harajin da suka kusa N18bn a hannun wani kamfanin NNPC, Petroleum Products Marketing Company (PPMC) Ltd,” Inji shi

Kara karanta wannan

Wasu Matasa Sun Kunno Wuta Suna Neman a Soke Zaban Sanata Mace a Najeriya

“Maganar gaskiya, PPMC ya ƙi da yarda hakan kuma ya ƙalubalance shi ta hanyoyin da suka dace."

Kakakin ya bayyana cewa gwamnatin jihar Ogun ta kai ƙara kotu kan lamarin inda yace hakan ba abin mamaki bane.

Ya ƙara da cewa lamarin yana gaban kotu, inda yace NNPC zata wanke kanta yadda yakamata a gaban kotun.

Hukumar EFCC Na Bincikar Wasu Ministiri 2 Kan Badakalar Kuɗi

A wani labarin na daban kuma, hukumar EFCC ta na gudanar da bincike kan wasu ministiri biyu na gwamnatin Buhari bisa zargin karkatar da akalar maƙudan kuɗaɗe.

Hukumar EFCC tace waɗannan ministirin biyu akwai rashin gaskiya sosai a cikin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng