An Harbe Dalibin Ajin Karshe a Jami'ar UNIBEN Har Lahira a Hostel
- An bindige ɗalibin jami'ar Benin da ke jihar Edo (UNIBEN) har lahira a ɗakin kwanan ɗalibai ranar Litinin
- Rahoto ya nuna cewa lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 9:00 na dare ya haddasa tashin hankali da tsoro tsakanin ɗaliban jami'ar
- Wani ɗalibi da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yadda maharan suka farmaki mamacin ba yadda za'ai ya tsira
Edo State - Wasu 'yan bindiga da ba'a sani ba sun harɓe ɗalibin jami'ar Benin (UNIBEN) da ke shekarar ƙarshe a karatunsa har lahira a ɗakin kwanan ɗalibai Hall 3 Hostel.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa alamu sun nuna lamarin ya yi kama da kashe-kashen ƙungiyoyin asiri a jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Marigayi ɗalibin wanda aka fi sani da 'Mayor' yana karantar kwas ɗin Public Administration a jami'ar kuma an harbe shi har lahira da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Litinin.
Lamarin ya haddasa tashin hankali da fargaba a tsakanin ɗalibai. A halin yanzun motar ujila ta ɗauki gawarsa zuwa ɗakin ajiyar gawarwaki na Asibitin koyarwa na UNIBEN.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani ɗalibin jami'ar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa jaridar Punch cewa maharan sun harbi marigayin a fuska.
A kalaman dalibin ya ce:
"Kisan ɗalibin ya haddasa tashin hankali, ɗar-ɗar da fargaba a makaranta. Har ta kai ga ɗalibai na tsoron zama a Hostel ɗin da abun ya afku."
"An harbe shi a kan fuska kuma ba bu wata dama da zai iya tsira da rayuwarsa a harin."
Duk wani yunkuri na jin martanin jami'ar ya ci tura domin har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton jami'in hulɗa da jama'a na UNIBEN, Dakta Benedicta Ehanire, bai amsa saƙonnin da aka tura masa ba.
Yan Sanda Sun Mamaye Sakatariyar Jam'iyyar Labour Party a Imo
A wani labarin kuma 'Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar Jam'iyyar LP, Sun Kwace Iko Nan Take
Jami'an hukumar yan sanda sun kwace iko da Sakatariyar LP da ke Owerri, babban birnin jihar Imo, kudu maso gabashin Najeriya.
Uwar jam'iyyar ta ƙasa ta koka kan abinda ya faru, tace wannan ba shi ne karo na farko ba.
Asali: Legit.ng