Orji Kalu: Tsohon Gwamna Kuma Fitaccen Sanatan APC Ya Yi Babban Rashi a Iyalansa
- Kowane rai zai ɗanɗani ɗacin mutuwa, Allah ya yi wa matar Sanata Orji Uzo Kalu, rasuwa tana da shekara 61 a duniya
- Kalu, tsohon gwamnan jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya ne ya sanar da rasuwar uwar gidansa a shafinsa
- Ya ce ta kasance mutumiyar kirki mai bautar Allah kuma za'a gudanar da bikin tunawa da ita a ƙasae Amurka
Abia - Tsohon gwamnan jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya, Sanata Orji Kalu, ya sanar da mutuwar uwar gidansa, Misis Ifeoma Kalu.
A wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu kuma aka wallafa a shafinsa na Facebook, Kalu ya ce matarsa ta farko ta koma ga mahaliccinta tana da shekaru 61 a duniya.
Tsohon gwamnan kuma mai tsawatarwa a majalisar dattawa 'Chief Whip' ya ce marigayya Ifeoma mace ce mai nagarta, wacce ta sadaukar da kanta wajen bauta wa Allah da taimakon mutane.
Sanatan ya bayyana cewa za'a gudanar da bikin tunawa da marigayyar na musamman domin girmamawa a ƙasar Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwan da ya wallaha a shafinsa, Sanata Kalu ya ce:
"Cikin nauyin zuciya da raɗaɗi mai zafi, muna sanar da mutuwar Misis Ifeoma Ada Kalu, mai kimanin shekaru 61 a duniya."
"Ta kasance mace ta gari a zamanin rayuwarta, wacce ta sadaukar da kanta wajen bauta wa Allah da taimaka wa al'umma. An shirya gudanar da bikin tuna wa da ita a ƙasar Amurka."
"Dan Allah ku riƙa sanya ta a Addu''inku da sauran abokai da masoyan da suka tafi suka barmu a wannan lokacin mai wahalar jurewa. Muna fatan ranta ya samu salama."
Sanata Orji Kalu na cikin shugabanni a majalisa da ke hangen kujerar shugaban majalisar Dattawa a majalisa ta 10 da ake dab da rantsarwa.
Yan ta'addan IPOB sun sheka barzahu a Abiya
A wani labarin na daban kuma Yan Ta'adda da Dama Sun Mutu Yayin da Suka Kaiwa Yan Sanda Hari a Abia
Rundunar yan sandan jihar Abiya ta ce jami'anta sun samu nasarar dakile yunkurin mambobin ƙungiyar 'yan awaren IPOB, sun sheƙe 5.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce mambobin ƙungiyar sun yi yunkurin kaiwa 'yan sanda hari amma mummunan nufin ya koma kansu.
Asali: Legit.ng