Mamman Daura Ya Karbi Bakuncin Zababben Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima

Mamman Daura Ya Karbi Bakuncin Zababben Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima

  • Zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya gana da na hannun daman shugaban kasa, Mamman Daura
  • Shettima ya bayyana dan uwan shugaban kasa Muhammadu Buharin a matsayin tsohon ubangidansa da suke bankin AIB
  • Da yake yi masa addu'an samun karin lafiya, Shettima ya kuma tuna yadda dangantakarsa da Daura ya fara kimanin shekaru 30 da suka gabata

Malam Mamman Daura wanda dan'uwa ne kuma na hannun daman Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Kashim Shettima, zababben mataimakin shugaban kasa.

Mataimakin shugaban kasar mai jiran gado shine ya bayyana labarin ganawar tasu wanda suka yi a karshen makon nan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na soshiyal midiya.

Mamman Daura da Kashim Shettima
Mamman Daura Ya Karbi Bakuncin Zababben Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima Hoto: @KashimSM
Asali: Twitter

Shettima ya bayyana Mamman Daura a matsayin ubangidansa a bankin kasa da kasa na Afrika wato AIB inda ya yi aiki a matsayin shugaban sashin kula da hada-hadar banki, reshen Kaduna.

Kara karanta wannan

'Matsalolin' Najeriya Na Hana Ni Barci, Har Na Kamu Da Rashin Lafiya, Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman

A wancan lokacin, Mamman Daura ne yake a matsayin Ciyaman na hukumar bankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya wallafa a shafinsa na Twitter:

"Na kai ziyarar bangirma ga mahaifina kuma tsohon ubangidana, Malam Mamman Daura (Durbin Daura).
"Dangantakata da Malam ya samo asali ne kimanin shekaru 30 da suka wuce lokacin da nayi aiki da Bankin kasa da kasa na Afrika (AIB) a matsayin shugaban sashin hada-hadar banki, reshen Kaduna inda shi kuma yake a matsayin ciyaman na hukumar bankin.
"Allah ya kara ma Baba lafiya, ameen."

Jama'a sun yi martani

@exboy10 ya ce:

"Aamin, Allah yayi riko da hannun ku wajen mulkin talakawa a Nigeria ."

@DahiruMaiha ya yi martani:

"Ko bayaso haka Allah yaso linzami tafi bakin Kura sir ."

@YUSUFSU86658615 ya ce:

"Ka fadawa mamman daura saura kiris."

@Muftahoolkhair ya ce:

"Sir Kashim wallahi ina kaunarka.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Fito Yayin Da Shettima Ya Gana Da IBB, Abdusalami Gabanin Rantsar Da Tinubu

"Ina fatan wata rana in hadu dakai."

@IsahSal15264590 ya yi martani:

"Masha Allah alhamdulillah may Almighty Allah help us ameen YA ALLAH alhamdulillah."

@HassanJada_ ya ce:

"Allah ya bada ladan ziyara. Iftaar Mubarak."

@khaliyu ya ce:

"Masha Allah."

@miibrahimhja ya ce:

"Masha Allah."

@IbrahimLimanti

"Masha Allah."

@jasadeeq044 :

"Masha Allah."

Shirin kafa gwamnatin wucin gadi: Babu abun da zai hana mika mulki, Primate Ayodele

A wani labarin kuma, fitaccen faston Najeriya kuma shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa babu abun da zai hana mika mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.

Primate Ayodele ya tabbatar da cewar ba za a yi nasarar kafa kowace gwamnati ta wucin gadi ba a Najeriya kamar yadda ya ce Allah ya nuna masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng