“Muna Alfahari Da Ke”: Dattijuwa Ta Samu Fiye Da Miliyan N44 Bayan Bidiyonta Ya Yadu

“Muna Alfahari Da Ke”: Dattijuwa Ta Samu Fiye Da Miliyan N44 Bayan Bidiyonta Ya Yadu

  • Wata ma'aikaciya mai suna Nola ta samu tallafin zunzurutun kudi har fiye da dala 100,000
  • Hakan ya kasance ne bayan an gano matar a cikin wani bidiyo da ya yadu a TikTYok zaune ita kadai cikin bakin ciki
  • Masu amfani da soshiyal midiya da suka ci karo da bidiyon a TikTok sun taimaka mata kuma zuwa yanzu sun tara mata fiye da $100,000

Wata ma'aikaciyar kamfanin Walmart, Nola, ta samu dalilin sake farin ciki a rayuwarta bayan ta samu kyautar kudi fiye da $100,000 (miliyan N44.3) daga wasu bayin Allah.

A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano dattijuwar matar zaune ita kadai a dakin hutu na Walmart, kuma hakan ya sa masoya tausaya mata.

Dattijuwa zaune cikin bakin ciki da kuma ita tsaye da wani
“Muna Alfahari Da Ke”: Dattijuwa Ta Samu Fiye Da Miliyan N44 Bayan Bidiyonta Ya Yadu Hoto: Dbon973_.
Asali: TikTok

Mai amfani da TikTok Dbon973_ ya wallafa bidiyon mai tsuma zuciya a dandalin dauke da taken:

Kara karanta wannan

“Sabon Sunana Hajia Meenah Mercy”: Daga Karshe Jarumar Fim Ta Tabbatar Da Shigarta Musulunci

"Bai kamata rayuwa ya yi wahala haka ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuni bidiyon ya yadu kuma an bude mata asusun GoFundMe don samun tallafi daga manyan mutane. Cikin awanni 24, an tara mata fiye da $100,000.

Dbon973_ ya kuma wallafa bidiyo mai tsuma zuciya inda ya hadu da Nola domin tura mata kudin jim kadan bayan nan.

"Sun ga cewa kina da kwazon aiki, shakka babu. Duk muna alfahari da ke, kuma muna so mu baki $110,000 wannan shine abun da muka tara maki," ya sanar da ita.

Sai dai kuma, da suke martani ga bidiyon, wasu sun caccaki matar inda suka yi ikirarin cewa yanayinta bai gamsar ba ko kadan.

Jama'a sun yi martani

@pabloriverab52:

"Dan uwa ana sa ran wani da ke da kamfani mai kyau zai iya ba mutumin nan aiki mai kyau, idan Walmart suka kore shi saboda wannan karamci nasa."

Kara karanta wannan

Jaruma Mai Kayan Mata: Sai An Biya N1m Ake Gani Na Ido-Da-Ido, Magana Ta Waya Kuma N250,000

@_zoeybowie_:

"Mutanen da na da tunani na daban idan aka zo maganar kudi. Bana tunanin abun da ta yi ba daidai bane, har zuciyarta ne. Abun ya burge."

@sweettartesss:

"Bata fahimci abun da ke faruwa ba, kakata za ta kai kamar haka. Ya yi maki kyau Nola kuma ina taya ki murna kan wannan."

Kalli bidiyon a kasa:

Yadda Allah ya tarbawa garin wani yaro da ke gararanba a titi nono

A wani labarin kuma, wani matashin yaro da ke kwana a titi ya samu tallafi daga wasu bayin Allah, inda a yanzu haka an dauki nauyin karatunsa zai tafi UK.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel