Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Bindiga 5, Sun Kwato Makamai a Kaduna

Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Bindiga 5, Sun Kwato Makamai a Kaduna

  • Hazikan sojoji sun yi gagarumin nasara a kan wasu yan bindiga da ke addaban garuruwa a jihar Kaduna
  • Dakarun sojin sun bude wa yan bindigar wuta a wani arangama da suka yi inda suka halaka mayaka shida
  • Daga cikin kayayyakin da aka kwato a hannun maharan harda babura, bindigogin AK 47, layoyi da sauransu

Kaduna - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wasu yan bindiga biyar da ke addaban wasu garuruwa a jihar Kaduna, jaridar The Cable ta rahoto.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Musa Yahaya, mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar sashi na 1, ya ce an kashe yan bindigar ne yayin arangama da sojojin a ranar Juma'a.

Taswirar jihar Kaduna da ke arewa maso yamma
Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Bindiga 5, Sun Kwato Makamai a Kaduna Hoto: Punch
Asali: UGC

Yahaya ya ce:

"Ta kokarin da ake na yaki da yan ta'adda da miyagu da ke addabar yankin arewa maso yamma, dakarun sun gudanar da aikin kakkaba a Kanti-Tantatu da ke dajin Kubusu, tsaunukan Kaso, da sauran yankuna a karamar hukumar Chikun da ke Kaduna.
"Yayin aikin wanda ya shafe tsawon awanni da dama, dakarun sun lallasa miyagun, inda suka kashe yan bindiga biyar."

An kwato makamai yayin arangamar

Ya kuma ce an gano bindigogin AK 47 guda hudu, kunamar bindigar AK 47 shida, alburushi 7.62mm 24, babura uku, adda daya, wayoyin hannu biyu da wasu layoyi daga wajen yan ta'addan.

Ya kara da cewar wannan aiki na dakarun ya hana miyagun katabus din yi abubuwa kuma ya dawo da zaman lafiya a yanzkin, wanda hakan ya dawo da harkokin tattalin arziki da kasuwanci.

Yahaya ya yi kira ga yan kasa masu bin doka da su ci gaba da tallafawa dakarun da sauran hukumomin tsaro da bayanai masu muhimmanci da zai taimaka a yaki da rashin tsaro, rahoton Punch.

A cewar sanarwar, Taoreed Lagbaja, babban kwamandan rundunar, ya yabama dakarun a kan aikinsu sannan ya bukace su da kada su yi kasa a gwiwa a aikinsu.

A wani labari na daban, mun ji cewa jami'an yan sanda sun kama shugaban inyamurai na yankin Ajao da ke jihar Lagas bayan ya yi barazanar kwaso yan haramtaciyyar kungiyar IPOB zuwa Lagas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng