Yadda Wani Tsoho Yayi Awon Gaba da Wayoyin Mutane 70 Cikin Kwarewa

Yadda Wani Tsoho Yayi Awon Gaba da Wayoyin Mutane 70 Cikin Kwarewa

  • An shigar da ƙarar mutumin ne ana zargin sa da aikata sibaran-nabayyen wayoyi 70 a wani wuri
  • Mutumin ya haɗa kai tare da wasu wajen aikata manaƙisar wayoyin cikin salon kwarewa irin na kwamushe
  • Darajar wayoyin daya ɗauka takai aƙalla miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar.

Wani matashin tsoho ɗan shekara 54 mai suna Innocent Udoh ya shiga hannu dumu-dumu a yayin daya bayyana a kotun tafi da gidanka dake lardin Iyaganku na garin Ibadan.

Shi dai wannan tsoho mai abin mamaki ya gurfana ne abisa zargin da ake masa na sace wayoyin salula guda 70 wanda darajar su takai kimanin Naira Miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai da ɗari biyar.

Wayoyi
Yadda Wani Tsoho Yayi Awon Gaba da Wayoyin Mutane 70 Cikin Kwarewa
Asali: UGC

Udoh wanda ba'a bayyana adireshin sa ba, ana tukumar sane da laifin sata tare da ƙitsa manaƙisa. Kamar yadda Dailypost ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana Saura Wata 2 Cikar Wa'adin Mulkin Sa, Wani Babban Ministan Buhari Yayi Murabus

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon da ake zargi da aikata wannan balahirar, yace bai aikata laifin da ake zargin sa ba.

Dan sandan da yake gabatar da wanda ake tuhuma ASP Sikiru Ibrahim ya shaidawa kotun cewar, Udoh da wasu mutane ne suka kitsa manaƙisar satar.

Satar an aiwatar da ita ne a ranar 30 ga watan Maris 12:00 na safe zuwa 5:00 na safe a Mokola, dake garin Ibadan.

Ibrahim yayi zargin cewa, tsohon da ake zargi da sace waya samfurin android na itel ta N750,000.

Tare da ɗauke wayoyi 20 kwance wadanda ba sababbi ba wanda suke android ne kuma darajar su takai naira Miliyan ɗaya, wanda wani ɗan kasuwa Nwaoma Ezeco ya mallaka.

Yace wannan laifi, ya saɓawa sashi na na 516 da sashi na 390 (9) na kundin dokokin jihar Oyo, na shekarar 2000.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

Alƙalin Kotun, Mrs T. B. Oyekanmi, ta bada belin wadanda ake zargi akan kuɗi N500,000, tare da gabatar da waɗanda zasu tsaya musu.

Mai shari'ar ta ɗage shari'ar har zuwa 26 ga watan Afrilu domin cigaba da sauraren ƙarar kamar yadda jaridar The Punch da suka rawaito.

Daga Yau na Daina Sata Inji Matar da take sata tun tana sa shekaru 7

A wani labari mai alaƙa da sibaran-nabayyen kayan mutane, da jaridar legit.ng ta kawo, wata mata yar ƙasar Ghana ta bayyana wani abu daya kaɗa mutane cikin kogin mamaki, sanda tace ta daina sata bayan ta daɗe tana yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar