Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

  • Zakzaky dai ya zargi DSS da ɗauke masa fasfon sa a shekarar 2018
  • Lauyoyin sa sun bawa mai Shari'a Justice Obiora shaidu 10 domin tabbatar da zargin
  • Justice Obiora tayi fatali da ƙarar, inda tace shaidu basu da inganci. Dalilin Zanga-zangar sakin Fasfo

Abuja - Da alama tsuguni bata ƙare ba ga mabiya Malam Ibrahim El-Zakzaky

Tun bayan da aka saki malamin, mabiyan sa suke ta gursheƙen faman ganin an bashi Fasfo din sa.

Wannan dalili yasa yanzu haka suka ƙara dira birnin tarayya Abuja, domin neman shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cirewa El-Zakzaky dokar hana shi fita waje da aka saka masa.

Zakzaky
Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky ɗin sa Hoto: Legit.ng
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Riƙe fasfon din bai tsaya akan Zakzaky ba, hattana matar sa, Malama Zeenah abin ya taɓa.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan 2023: Taya Murnar Nasir Yusuf Gawuna Ga Abba Kabir Yusuf Gida-Gida

Fasfon ɗin dai idan an basu, suna iƙirarin zasuyi amfani dashi ne wajen fita ƙasar waje domin neman magani.

Abinda Gwamnatin Najeriya tace, taƙi wayon, domin kuwa ta gano dabarar su, saboda haka da sake.

A wani zama da tayi a Abuja, wata babbar kotu tuni ta shaida cewa buƙatar bawa Zakzaky da matar tasa Fasfo bazai samu ba.

Kotun ta umarci ƴan sandan farin kaya na Najeriya dasu cigaba da ajiye fasfon malamin da matar sa har sai lokacin daya kamata a bashi.

Da take zartar da hukuncin mai Shari'a Justice Obiora, ta yanke hukuncin cewa, Lauyoyin na Zakzaky sun kasa miƙa shaidu ƙwarara da zasu tabbatar da cewa, Fasfo ɗin sa ya ɓata.

Sun dira kotun, domin su nuna cewa hakika DSS ta ɗaukar masa Fasfo tun a shekarar 2018 lokacin daya dawo daga India kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: 'Yadda Aka Mun Tayin Makudan Kuɗi da Barazanar Kisa Na Canja Sakamakon Zaben Gwamna'

Yan Shi'a 6 da Jami'an Tsaro Suka Bindige a Zaria

A wani labari daya wuce wanda jaridar legit.ng ta ruwaito tace shugaba ga ƙungiyar Shi'a ta zaria ya bayyanawa manema labarai jerin sunayen su da suka rasa rai a tattakin Zariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar