Munanan Haduran Mota Sun Janyo Asarar Rayuka a Jihar Bauchi
- Wasu munanan haɗura da suka auku a jihar Bauchi sun janyo asarar rayukan mutane da dama
- Munanan haɗuran motar sun yi sanadiyyar rasuwar mutum tara yayin da wasu daban kuma suka raunata
- Hukumar kiyaye aukuwar haɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar itace tayi ƙarin haske kan haɗura biyun da suka auku
Bauchi- Mutum tara sun rigamu gidan gaskiya a wasu munanan haɗuran mota da ya ritsa da wasu motoci uku a wurare daban-daban a jihar Bauchi.
Hukumar kiyaye aukuwar haɗura ta ƙasa (FRSC) ta jihar Bauchi, itace ta tabbatar da hakan.
Haɗarin farko a cewar rahoton Zebra 30, FRSC Toro- Magaman Gumau, ya auku ne a ranar Laraba 29 ga watan Maris, 2023 da misalin ƙarfe 6:25 na safe wanda aka kawo rahoton sa da misalin ƙarfe 6:30 na safe sannan jami'an hukumar suka isa wajen da misalin ƙarfe 6:30 na safe.
Haɗarin ya auku ne a Panshanu akan hanyar Bauchi zuwa Jos a tsakanin wata mota ƙirar Toyota Hiace mai ɗauke da rajistar KGG 26 LG da wata mota ƙirar Peugeot Boxer J5, wacce bata ɗauke da lamba. Rahoton Tribune
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mutum 5 dukkanin su manyan maza ne suka rasu a haɗarin inda suka ƙone ƙurmus saboda wutar da ta kama a dalilin fashewar tayar mota da ƙwacewar tuƙi.
Tun da farko hukumar FRSC, a ofishin ta na Dass ta kawo rahoton mutuwar mutum huɗu yayin wasu mutum biyar suka jikkata a wani mummunan haɗarin mota. Rshoton Daily Post
Mummunan haɗarin motar ya auku ne a ranar Litinin, 27 ga watan Maris 2023, a gadar Bagel ta kan titin babbar hanyar Bauchi zuwa Dass.
Haɗarin ya ritsa da mutum 9, takwas daga ciki maza sai mace ɗaya. Sannan mutum huɗu dukkanin su maza suka rasu a haɗarin, yayin da mutum biyar huɗu maza sai mace ɗaya suka samu munanan raunika.
Masha Allah: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Rijiyar Hakar Man Fetur a Jiha Ta 2 a Arewacin Najeriya, Ta Bayyana Burin Ta Akan Rijiyar
Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger
A wani labarin na daban kuma, rayuka da dama sun salwanta a wasu hadarurruka da suma auku a jihar Niger.
Haduran sun ritsa ne da wasu motocin zirga-zirga na yau da kullum.
Asali: Legit.ng