INEC Ki Sake Zaben Gwamna Na Jihar Kaduna – Masu Saka Ido

INEC Ki Sake Zaben Gwamna Na Jihar Kaduna – Masu Saka Ido

  • Masu saka ido akan zabe a Kaduna sunce zaben kaduna ya samu tasgaro da bazai maida wanda aka ayyana yaci zabe a sahihin zababben gwamna ba
  • Hadakar masu saka ido akan zaben tace, an gudanar da zabe lafiya kalau a jihar Kaduna kamar yadda aka tsara
  • Amma lamarin ya canja da aka zo tattara sakamakon zaben, bayaga wasu kananan hukumomi da ba’a tura sakamakon zabe ta IREV ba

Abuja - Hadakar masu saka ido domin gudanar da zabe sahihi sunyin kira ga hukumar zabe ta Kasa da sake duba na tsanaki ga sakamakon zaben gwamnan jihar da aka kammala.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewar masu saka ido a zaben sun ce tabbas zaben anyi sa lafiya kalau a jihar amma wajen tattara sakamako cike yake da kusakurai idan aka hada da abinda aka daura akan manhajar INEC ta IReV.

Kara karanta wannan

"INEC Ta Yi Kuskuren Ayyana Abba Gida-Gida Matsayin Zababben Gwamnan Kano", Masu Sa Ido Kan Zabe

Baturen zabe dai na jihar , Farfesa Lawan Bilbis, ya ayyana cewar, dan takarar jam’iyyar APC, Uba Sani ne yayi nasara da kuri’u 730,002.

Ine Irev
INEC Ki Sake Zaben Gwamna Na Jihar Kaduna – Masu Saka Ido Hoto:Legit.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Inda daga bangare guda kuma abokin karawar sa na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 719,196.

Sakamakon zaben ya nuna cewar, APC tasamu nasararta ciki garuruwa guda goma ne The cable.

Yayin da sakamakon ya nuna PDP ta samu tata nasarar cikin garuruwa goma sha uku.

A wani kwarya-kwaryan taron manema labarai a Abuja, shugaban masu saka ido na kasa,

Romans Azubuike ya shaidawa jaridar Thisday cewar:

“Muna kira ga INEC da ta sake duba zaben nan na jihar Kaduna”.
“Zaben an zuba shi a fai-fai kowa yana gani, har sai da akazo tattara sakamako sannan abubuwa suka canja. Haka abin yake a farko tabbas; musamman ma a Kaduna ta Kudu, Birnin Gwari, da sauran kananan hukumomi da suka gaza daura sakamakon zaben su a manhajar INEC kai tsaye dagas wajen zaben”. Inji sa.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Dan takarar gwamnan NNPP a Arewa ya ce bai amince da sakamakon zabe ba, zai tafi kotu

An Bayyana Abubuwan Kalubale da Tinubu Yake Fuskanta a Zagaye Dashi Bayan Ya Cika Shekara 71

An wani labari mai kama da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, an bayyana abubuwan da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke yake fuskanta na kalubale.

Hakan na zuwa ne bayan ya cika shekaru 71 a duniya, a ranar 29 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar