Yin Bilicin: Matan Najeriya Kaso 77% Dake Bilicin, Duk Suna Fuskantar Hadarin Sankarar Mama

Yin Bilicin: Matan Najeriya Kaso 77% Dake Bilicin, Duk Suna Fuskantar Hadarin Sankarar Mama

  • Najeriya ita ce kasa ta farko a Afirka da kaso 77 cikin dari da matan kasar suka fi yin amfani da mai dake canja fasalin fata
  • Kasar Togo ce ke biye mata baya da kaso 59, Afurka ta Kudu kaso 35 , sai kuma Senegal mai kaso 27 a cikin dari
  • Kadan daga illolin mai dake canja fasalin fata sun hada da taba sashi masu matukar amfani na jikin mutum

Lamarin "Blicin" yana nema ya zama ruwan dare gama duniya, baga mazan ba, baga matan ba.

Yayin da lamarin na canja fasalin fata ke kara ta'azzara a Najeriya, hukumomi sun shigo tare da fara fadakarwa domin magance matsalar kafin ta zama kadangaren bakin tulu.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) tana jan hankali akan yadda mutane ke cigaba da yin amfani da man, inda tace masu amfani da shi ka zasu kamu da cutar sankarar mama idan har basu daina ba.

Kara karanta wannan

A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

Nafdac
Yin Bilicin: Kaso 77 na Matan Najeriya Na Fuskantar Hadarin Sankarar Mama Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar tana magana ne akan wani rahoto na baya bayan nan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar wanda ke nuni da da cewar, kaso 77 na matan Najeriya nayin amfani da samfurin mai da yake canja launin fata akaio-akai.

NAFDAC tayi wannan kiran ne jiya litinin a yayin rantsar da shirin da take na wayar da kan mutane akan hatsarin yin amfani da man canja launin fata a can Abeokuta dake yankin kudu maso kudu na Najeriya.

Babban Daraktan hukumar, farfesa Moji Adeyeye, ta samu wakilcin Daraktan Kima da Bincike na hukumar Dr. Leonard Omokpariola.

Tace yin amfani da mai dake canja launin fata da ire-iren mayuka irin su ka iya taba sashi masu matukar amfani na jikin mutum, baya ga kaikayi, rashin lafiyar jiki, borin fata, kurjewar fata, tsufa na gaggawa, da kuma rashin warkewar ciwo da wuri.

Kara karanta wannan

“Allah Madaukakin Sarki Ya Amshi Sadaukarwarmu”: Jarumar Fim Ta Koka Kan Gwagwarmayar Matar Musulmi Yayin Ramadan

Tace:

"A shekarar data gabata, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha yayi aiki akan wani kudirin majalisar dattawa, ya rubutawa NAFDAC bukatar da take da akwai na daukan mataki kwakwkwara domin samun mafiita daga tushe akan wannan lamari mai hatsarin gaske daya ratsa ko ina a cikin mutanen Najeriya, watau amfani da mai mai canja launin fata".

Jaridar The nation ta ruwaito yadda taci gaba da cewa:

"Da wurwuri muka dauki mataki mai kyau na gaggawa wajen wayar da kan al'umma ta kafofin sadarwa, hukumomi masu sawa a daina safarar kayan ta hanyar amfani da bayanan sirri, wanda haka yasa muka kwace kaya masu yawa sannan muka kona kayan".
"Bayanai na hukumar lafiya ta duniya na 2018 ya tabbatar da cewa, man canja launin fata ya zama ruwan dare gama duniya, cikin matan Najeriya kaso 77 cikin 100 na amfani da wannan mai wanda muka fi kowacce kasa yi, idan aka hada data kusa damu wato Togo mai kaso 59, Afurka ta Kudu kaso 35 , sai kuma Senegal mai kaso 27 a cikin dari".

Kara karanta wannan

Toh fa: DSS ta hango matsala a Najeriya, ta ba 'yan kasa shawarin kariya

WHO Ta Ayyana Kyandar Biri a Matsayin Wanda Ke Bukatar Daukin Gaggawa a Duniya

Hukumar dake sanya ido akan lamurran lafiya na duniya WHO ta saka cutar ƙyandar burrai a cikin jerin cututtukan dake ɓukatar a ɗaukar mata mataki na ujila.

Tedros Ghebreyesus, wanda yake shine shugaban na hukumar, ya bayyana haka ranar Asabar yace cutar na yaɗuwa ta sababbin hanyoyi da ake kokarin ganowa.

A Najeriya, NCDC ita ce kat, a kula da cuta irin wadannan, tuni ta bayyana cewar aƙalla mutane 101 suka kamu a wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar