A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

  • Jihar Niger ta fuskanci hadarurruka wadanda suka faru daban daban a karshen satin daya gabata
  • 25 ga watan Maris, 2023 an samu hatsari akan hanyar Minna-Lapai ta Kauyen Tungar Mallam inda mutane 3 suka rasa rayuka
  • Wasu ababen hawa guda biyu sun kara gauraya masu dauke da mahaya guda 13, inda aka kai 10 asbiti. Hukumar kula da hadurra ta kasa ta ala-kanta lamarin da gajiyar direbobi

Niger - Idan ajali yayi kira, koda a birnin Sin ne dole mutum yaje wurin.

Jihar Niger ta hadu da wasu jerin gwanon hadarurrukan da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da adadin su ya tayar wa 11 a wurare daban daban na jihar.

Lamarin maras dadin ji ya afku ne a karshen satin nan, yayin da wasu motoci suka yin lodin fasinja domin zuwa wuraren nema kamar yadda aka saba yau da kullum.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Niger Accident
A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger Hoto: Blueprint Asali: UGC
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Blueprint ta ruwaito yadda mutane maza magidanta guda 5 tare da yara guda 2 da kuma wata mace guda daya suka ruga mu gidan gaskiya a wani taho-mugama da wata tirela tayi a kauyen Chigi dake kan hanyar Kudu – Mokwa ranar 23/3/2023.

Wannan mummunan taho mugama daya faru yasa mutane 32 da biyu samun mabambamtan munanan raunuka a sassan jikkunan su.

Rahotanni sun kara nuna yadda wani hatsari ya faru a ranar 25 ga watan Maris 2023, akan hanyar Minna-Lapai ta Kauyen Tungar Mallam, wanda shima ya lamushe rayuka guda 3.

Haka kuma duk dai a jihar ta Niger, wasu ababen hawa guda biyu sun kara gauraya, ababen hawan dake dauke da mahaya guda 13, 3 daga ciki basu samu rauni ba yayin da aka garzaya da guda 10 zuwa asibiti mafi kusa.

Kara karanta wannan

25 Sun Mutu, 10 Sunji Munanan Raunuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Bauchi

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hukumar kula hadurra ta kasa reshen Lapai din ta Niger, ya tabbatar da lamarin ya faru a daidai karfe 3:50 na yamma a ranar 25/03/2023, inda ya tabbatar da cewa, hatsarin ya faru ne sakamakon gajiyar da direbobin suka yi.

An Bukaci Muhammadu Buhar Ya sanya Hannu akan Wata Muhimmiyar Doka

Anyi kira ga shugaba Buhari daya saka hannu akan dokar da zata halasta Hukumar Bijilanti kafin karewar mulkin sa.

Kiran na zuwa ne ta bakin babban shugaban kungiyar ta kasa dake birnin Abeokutan Najeriya. Shugaban nay an bijilanten ya bayyana cewa, sahalewa kungiyar ta zama hukuma mai yanci da doka zata gane ba karamin amfani zai kawowa kasar ba ta bangaren tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar

Tags: