Gobara Ta Lakume ATM Guda 3 a Wani Bankin Zamani a Jihar Kano
- An sake samun tashin gobara karo na barkatai cikin mako guda a garin Kano da ke arewa maso yammcin kasar
- Gobara ta kona na'urorin cire kudi na ATM guda uku kurmus a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano
- Lamarin ya afku ne a ranar Talata, 14 ga watan Maris bayan wasu wayoyin wuta sun hadu da juna daga cikin na'urorin
Kano - Mummunar gobara ta kona na'urorin cire kudi wato ATM guda uku na bankin Zenith da ke hanyar Tafawa Balera a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano a ranar Talata, 14 ga watan Maris, Vanguard ta rahoto.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin watsa sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya saki a garin Kano.
Abdullahi ya bayyana cewa hukumar ta kwana-kwana sun samu kira mai cike da damuwa da misalin karfe 12:06 na rana daga wani Ghali Muhammad cewa ana gobara a na'urorin ATM.
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Da samun kiran, sai muka gaggauta tura jami'anmu da motocin kashe gobara zuwa wajen da lamarin ke faruwa da misalin 12:11 na rana don kashe wutar don kada ya yadu zuwa sauran na'urorin na ATM."
Haduwar wayoyin wuta daga na'urorin ATM ne ya sababa gobarar, Hukumar kwana-kwana
Abdullahi ya kuma bayyana cewa ATM uku ne suka mutu kurmus sakamakon annobar, yayin da sauran ukun suka dan taba kuna kadan.
Ya alakanta gobarar da haduwar wayoyin wuta daga na'urorin ATM din, rahoton Aminiya.
Gobara ta tashi a kasuwar Singa ta Kano, ta yi barna mai matukar muni
A wani lamari makamancin wannan, a farkon makon nan ne mummunar gobara ta tashi a kasuwar Singa wacce ta yi suna wajen siyar da kayan abinci a garin Kano.
Gobarar da ta shafe tsawon dare har zuwa wayer gari tana ci ta lakume shaguna masu yawan gaske inda yan kasuwa suka tafka mummunar asara na miliyoyin naira.
Wasu daga cikin yan kasuwar sun samu kwashe yan abun da ya yi saura daga dukiyoyinsu kafin wutar ya yadu zuwa sauran kayayyakin shagunan nasu.
Asali: Legit.ng