“Ana Ba Kudi”: Dan Najeriya Ya Gano Buhuhunan Tsoffin Kudi Da Aka Nika, Bidiyon Ya Yadu

“Ana Ba Kudi”: Dan Najeriya Ya Gano Buhuhunan Tsoffin Kudi Da Aka Nika, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani matashi a Lagas ya yi ikirarin cewa ya gano buhuhunan tsoffin kudi da CBN ya watsar
  • Bidiyon nikakkun tsoffin kudin ya haddasa cece-kuce sosai saboda halin da ake ciki na karancin tsabar kudi
  • Bisa doka babban bankin Najeriya tana lalata takardun kudi marasa amfani lokaci zuwa lokaci karkashin kulawar tsaro

Wani mutumi ya gano damin tsoffin takardun naira da ake zargin Babban Bankin Najeriya (CBN) ne ya watsar da su.

Bidiyon wanda ya yadu a soshiyal midiya yana tashe a daidai lokacin da ake fama da rashin tsabar kudi a kasar.

Gwamnan CBN da nikakkun kudi
“Ana Ba Kudi”: Dan Najeriya Ya Gano Buhuhunan Tsoffin Kudi Da Aka Nika, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @cbn @instablog
Asali: Facebook

Cikin nikakkun bandir-bandir din kudin harda N500 da N1000 wacce kotun kolin kasar ta yi umurni da a ci gaba da amfani da su har zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2023.

A cikin bidiyon, an gano mutumin yana ihu:

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Manyan Arewa Sun Fada Wa Shugaba Buhari Abinda Zai Faru Idan Ya Ki Bin Umarnin Kotun Koli

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sun nika kudin, kun ga dukka wannan kudi ne, kudi da nake nema."

Jama'a sun yi martani

@obbydave ya rubuta:

"Kawai mutane na yin bidiyoyi suna wallafawa ba tare da samun dalili ba. Shin ya san dalilin da yasa aka nika su? Kowace kasa na nika takardun kudi don tattalin arziki. Yana taimakawa wajen daidaita tsadar kaya a kasa."

@stephen_ogugua ta rubta:

"Da kamata ya yi ace CBN ta kona su ba wai ta zubar da su a yanayin nan ba ko don tnutsuwar hankalin talakawar kasar."

@sami_oamen ya yi martani:

"Shin CBN ya fara nika tsoffin kudi ne, saboda ni ban fahimta ba."

@TundeJamiu5 ya ce:

"CBN karkashin Emefiele. Shine mafi muni kuma mutum mai rawan kai. Ka buga sabbin kudade yan kadan. Kai ba mai kishin kasa bane. Mutane na wahala.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Masani ya fadi kura-kurai 5 da CBN ya yi wajen kawo batun sauyin Naira

@Jojo_Amandy

"Kudade basa tsayawa har abada. Abu ne da CBN ya saba yi kakkabe lalatattun kudi, yagaggun kudi daga tattalin arziki, nika su ko kona su. Haka kuma, a wannan lokaci da aka sauya kudi, ana tsammanin haka."

Sauya kudi: Kungiyar ACF ta gargadi Buhari kan kin bin umurnin kotun koli

A wani labarin kuma, kungiyar tuntuba ta arewa wato ACF, ta ja hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kin bin umurnin kotun koli game da sauya fasalin kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng