"Ku yafe min dan Allah": Inji Direban Motan da Yayi Kicibis da Jirgin Ƙasa a Lagos Mutum 6 Suka Mutu
- Mahaya motar bas ɗin da suka tsira suna zargin Direban da yin kemadagas da gargaɗin karya tsallaka titin Jirgin ƙasan
- Sunce direban ya sanya abin jin sauti a kunnen sa, ya nanawa mota wuta, ya tunkari titin jirgin duk da gargadin yalo-fifa
- Gamuwar motar da jirgin aka ji wani sauti tamkar aradu zata faɗo, direban ko ƙwarzane baiyi ba, amma mutane 6 sun mutu
A ranar Alhamis ɗin data gabata ne dai aka haɗu da wani iftila'in taho mu gama da jirgin ƙasa da motar bas a Lagos.
Hatsarin da yayi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane shida, tare da jikkata gommai.
Direban motar da haɗarin ya rutsa dashi mai suna Oluwaseun Osinbajo, ya roƙi gafara da neman yafiya daga waɗanda abin ya rutsa dasu da kuma wadanda ya shafa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tunda da fari dai, mahaya motar bas ɗin sun zargi matuƙin motar dake da shekaru 44 a duniya akan kada ya tsallaka titin amma yaƙi.
Sun ce yana sanye da abubuwan jin sauti a kunnuwan sane, yayin da yake tukin kuma yayi ƙemadagas da umarnin da masu bada hannun titin jirgin ƙasan suka yayi masa akan ya tsaya.
Direban mai suna Osinbajo, yace motar ce birkin ta ya ƙi ci shi yasa ya kasa tsayawa.
Direban da yake aiki da ma'aikatar sufuri ta jihar Lagos, tuni aka maida shi sashen binciken manya laifuka na SCID bayan tsira da yayi daga hatsarin batare da yaji ko ƙwarzane ba daga hatsarin.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, ta jiyo Direban yana faɗawa ƴan uwan sa cewar:
"Ba laifi na bane. Tayaya zan ƙi sauraren gargaɗin masu kula da hanya?
"Ina rokon kowa da kowa, da a taimaka a yafe min, dan Allah."
Sojojin Najeriya Sun Tsinkayi Caji Ofis Cike Da Ƴan Sanda Tare da Gyarawa Wani ɗan Sanda Zama
Wannan diramar mai ban takaici da dariya ta faru ne a wani gari dake can jihar Delta, Kudu Maso Kudancin Najeriya.
An hangi vidiyon Lamarin mai daƙiƙa 30, ya nuna yadda ɗan sandan ya kasa zaune, ya kasa tsaye. Yan uwan sa suna lallashin sa, wanda alamu ke nuna ya dibi kashin sa a hannun sa.
Yayin da wani ɗan sanda yace abashi hayaƙi mai sanya hawaye domin ya tasar wa sojojin da suke ƙoƙarin kiran waya.
Asali: Legit.ng