Ramadan: Malamin Addini Yayi Kira Ga CBN a Saki Takardun Kuɗi Isassu

Ramadan: Malamin Addini Yayi Kira Ga CBN a Saki Takardun Kuɗi Isassu

  • Gari babu kudi, yayin da Ramadana yake kara gabatowa, masallata na bukatar kudi da yake na zahiri domin sayen kayan shan ruwa da sadaka
  • Hakan tasa Shahararren malamin addinin Muslunci nan mai suna Nurul Yaqeen na masallacin Jumma’a dake Life Camp, Abuja yayi kira da asaki kudi wa mutane
  • Nuru ya lissafa samun lafiya, gyaruwar addini da ɗabia , ruhi, hankali da mu'amala tsakanin mutane amatsayin kaɗan daga amfani da ake samu a watan Ramadana mai albarka

Abuja - Yayin da watan Ramadana mai albarka ke ƙara ƙaratowa, mutane na cigaba da kiraye kiraye ga babban bankin Najeriya daya ci gaba da sakin kuɗi isassu domin walwala.

Ɗaya daga cikin mutanen dake kiranye kiranyen sun haɗa da shahararren malamin addinin Muslunci nan mai suna Nurul Yaqeen na masallacin Jumma’a dake Life Camp, Abuja.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Jami'an Tsaro Wuta, Da Yawa Sun Mutu a Kaduna

Malamin yayi kira ga bankin ne da ya saki isassun kuɗaɗe sababbi duba da yadda watan Ramadan mai albarka yake tunkarowa.

Cash ne
Ramadan: Malamin Addini Yayi Kira Ga CBN Data Saki Takardun Kuɗi Isassu Hoto: UGc

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Al-Yolawi yayi kiran ne a yayin da yake huɗubar juma'a akan maudu'in "Amfanin Azumin Watan Ramadan: Ga Lafiya, Mu'amala, Hankali da Ruhi " ranar juma'a a Abuja.

Malamin yace, musulmi suna kashe kuɗi sosai a watan Ramadan wajen sayen abinci da kayan da zasuyi sadaka dasu, wanda yake faruwa sakamakon tsari, shiri na kasafin kudin aljihu akan yadda za'a kashe su.

A cewar sa:

"Hakan ya ta'allaƙa da yadda kuɗi yake shiga da fita daga hannun mutane ɗaiɗaiku da ƙungiyoyi, kuma hakan nada muhimmanci sosai ga harkar saye da sayarwa. Ci gaba da wanann salo, bayan ramadan yana da tasiri sosai wajen haɓaka kasuwancin ku".
"Inaso nayi amfani da wannan damar wajen kira ga gwamnatin tarayya da CBN wajen sakin isassun takardun kuɗi, domin watan Ramadan yana tunkaro mu gadan-gadan.

Kara karanta wannan

Tsakanin Hukumar Hisban Jihar Kano Da Matasa Yan TikTok

Ya ƙara jajjadadawa kamar haka:

"Domin mutane na matuƙar buƙatar kudi domin siye siyen Ramadana da sauran ƴan kunji kunji na yau da gobe...".

Malamin ya ƙara da cewa, masallacin nada niyyar yin ayyuka da yawa a watan mai kamawa, kama daga Taraweeh, Tahajjud, da Tafseer. Sai kuma ciyar da aƙalla Mutane 200 kullum har watan ya wuce.

Yayi kira ga waɗanda suke ƙoƙarin ganin sun taimaki tsarin dasu kawo tallafin a wajen da ake ibadar ko kuma su cilla kuɗi ta asusun masallacin domin samun gwagwgwaɓen lada.

Malamin kuma yayi bayanin cewa, Ramadana lokaci ne na tuba, azumi, kyautatawa, maida hankali kan ibada, tare da bada gudunmawa ga yan uwa musulmi a duk inda suke a duniya, duba da kasancewar sa daya daga cikin shika -shikan musulunci.

Jaridar Vanguard ta ruwaito yadda malamin ya lissafa samun lafiya, gyaruwar addini da ɗabia , ruhi, hankali da mu'amala tsakanin mutane amatsayin kaɗan daga amfani da ake samu a watan mai albarka.

Kara karanta wannan

Zagon Ƙasa: An Gurfanar Da Wani Ma'aikaci Gaban Kotu Bisa Sama Da Faɗi Da Miliyoyin Kuɗaɗen Kamfani

Hukumar NDLEA Ta Soma Daukar Aiki: Ta Lissafa 7 Sharruda Ga Masu Niyyar Nema

An buƙaci sababbin waɗanda suka kammala karatu su gwada sa'ar su wajen neman aiki a hukumar yaƙi da fataucin miyagun kwayoyi na NDLEA a shafinta na yanar gizo gizo.

A wani saƙo da hukumar ta sanar, tace ƴan Najeriya zasu iya nema da kwalin Sakandire, Polytechnic da kuma kwalin jami'a domin zama ma'aikatan hukumar.

Hukumar ta tabbatar da hakan ta shafin ta na Twitter ranar juma'a, 10 ga watan Maris. Inda tace kyauta ne neman ba ko sisi da za'a fitar daga aljihu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida