A Cigaba Da Hada-Hada Da Tsaffin N1000 da N500, CBN Yayi Tsokaci
- Mai magana da yawun CBN yace yan Najeriya su cigaba da harkokinsu da tsaffin kudadensu
- Duk da bankin CBN bata fitar da umurni ga bankuna ba, rahotanni sun nuna cewa sun fara fitar da kudaden
- A makon da ya gabata kotun koli tayi watsi da wa'adin da gwamnan CBN ya sanya na daina amfani da tsaffin kudi
Babban bankin Najeriya CBN ya umurci bankuna su cigaba da karbar tsaffin takardun kudin N500 da N1000 hannun yan Najeriya.
Hakazalika ya sanar da daukacin yan Najeriya su cigaba da hada-hada da tsaffin takardun kudinsu.
Ya ce yanzu ya halasta a cigaba da amfani da kudi bisa umurnin kotun kolin Najeriya, rahoton TheNation.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kakakin bankin CBN, Isa Abdulmumin, yace tuni bankuna sun fara baiwa mutane tsaffin kudi ta na'urorinsu na ATM duk da CBN bai bada umurnin haka ba.
Yace har yanzu bankin bai fitar da jawabi kan lamarin ba amma yan Najeriya zasu iya cigaba da hada-hada da tsaffin kudadensu bisa umurnin kotun koli.
A hirar da yayi da jaridar TheCable ta ruwaito, Abdulmumini yace:
"Bankuna na biyan tsaffin kudi da sabbin kudi. Dukka halas ne a doka."
"CBN ba fitar da jawabi bisa lamarin ba tukun. Duk bankin da ya baka kudi za ka iya karba."
Abdulmumin ya bayyana alhininsa bisa yadda yan Najeriya musamman yan kasuwa ke kin karbar tsaffin kudi.
Yace a cigaba da karba tun da kotu ya halasta.
Ya kara da cewa:
"A'a su daina kin karba. Dukkan halas ne a doka."
Wakiliyar Legit ta tattauna da wani ma'aikacin bankin UBA, Isuhu Abdul, wanda yayi tsokaci kan lamarin cewa bankuna sun fara fitar da tsaffin kudin.
Mr Abdul ya bayyana cewa bankinsu dai ta UBA bata fara ba.
A cewarsa:
"Bankin UBA bata fara fitarwa ba a sani na amma mun samu labarin bankin Zenith sun fara."
Ma'aikatan Banki Na Karbar Cin Hanci Daga Kwastamomi Yayin da Ake Fama Da Dogon Layi
A wani labarin kuwa, ana zargin ma'aikatan banki na ribatar karancin kudin da ake ciki.
An ce sun fara karbar kudi hannun mutane domin sanya cikin layin karbar kudi.
Asali: Legit.ng