"CBN Ne Ya Bamu Umarni" Bankuna Sun Fara Baiwa Mutane Tsohon N500 da N1000 a Legas
- Babban bankin Najeriya ya sahalewa bankuna su ci gaba da baiwa mutane tsoffin N200, N500 da N1000
- Mai magana da yawun CBN, Isa Abdulmumin, ya ce tsoho da sabon naira zasu ci gaba da yawo hannun jama'a
- Bincike ya nuna bankuna sun fara zuba tsoffin kuɗin a ATM kuma su na biya da su a kan Kanta
Lagos - Wasu bankunan kasuwanci a jihar Legas sun fara biyan kwastomominsu kuɗi da tsoffin takardun N500 da N100 a na'urar zare kuɗi ATM da kuma kan Kanta.
The Cable ta tattaro cewa hakan ta faru ne a yunkurin biyayya ga umarnin Kotun koli, wanda ta tsawaita wa'adin halascin amfani da kuɗin zuwa karshen watan Disamba.
Wani bincike da jaridar ta gudanar ranar Talata ya nuna cewa wasu bankunan kasuwanci sun fara ɗa'a ga umarnin Kotu, duk da shirun CBN da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
CBN ya amince da hukuncin Kotu
An tattaro cewa reshen bankin Zenith da ke yankin Festac Town ya ci gaɓa da biyan mutane da tsohon naira a kan Kanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"CBN ya amince tsoffin takardun kuɗin su ci gaba da yawo hannun jama'a har zuwa 31 ga watan Disamba, 2023, bisa haka ne muka fara baiwa mutane," inji wani ma'aikaci a Bankin.
Wani ma'aikacin bankin na daban kuma ya ce, "Umarni ya riske mu daga sama cewa mu biya buƙatun kwastomomin mu da tsoffin naira."
Haka zalika ATM ɗin Bankin UBA da ke kusa da Agege-Pen Cinema Bridge da kuma GT Bank na Ikeja, duk sun fara biyan mutane da tsohon naira sa'ilin da wakilin The Cable ya je wurin.
Ya halatta amfani da tsoffi da sabbin naira - CBN
Mai magana yawun CBN, Isa Abdulmumin, ya ce dukkan tsoffi da sabbin takardun naira zasu ci gaba da amfani kuma tuni bankuna suka fara baiwa kwastomomi.
Amma ya ce har yanzun babban bankin Najeriya bai fitar da sanarwa a hukumance ba.
"Bankuna na biyan tsoffi da sabbin naira, dukkan su suna da halascin amfani," inji kakakin CBN.
"Eh haka ne, har kawo yanzun CBN bai fitar da sanarwa a hukumance ba, amma duk wanda Bankuna suka baku ku karɓa, muna son sauƙaka kuncin 'yan Najeriya."
Abdulmumini ya nuna damuwa kan yadda wasu 'yan kasuwa ke ƙin karban tsoffin kuɗi, inda ya ƙara da cewa, "Bai kamata su ki karɓa ba, suna da halaccin amfani."
A wani gefen kuma mun samu labarin wasu Bankuna a Abuja da Kano sun bi Umarnin Kotu wajen baiwa mutane tsohon kuɗi
Sai dai duk da haka akwai wasu bankunan da N200 kacal suke bayarwa, a ceqarsa ba su samu umarni daga sama ba.
Asali: Legit.ng