Mutum 10 Yan Gida Daya Sun Mutu a Hatsarin Mota a Hanyarsu Ta Dawowa Daga Biki a Kano
- Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane 10 yan gida daya a hanyar titin Kaduna-Kachia
- Mamatan na hanyarsu ta komawa Kachi, jihar Kaduna bayan sun halarci bikin aure a mahaifarsu ta jihar Kano
- Motar mamatan, manya takwas da yara biyu ta yi tawo mu gama da wata motar daukar kaya
Kano - Wasu mutane 10 yan gida daya sun rasa ransu sakamakon hatsarin mota a hanyar babban titin Kaduna-Kachiya yayin da suke dawowa daga wani biki da suka halarta a jihar Kano.
Mummunan hatsarin ya afku ne a kusa da wani kauye mai suna Makyerri kusa da Idon a hanyarsu ta zuwa garin Kachia da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Lahadi, 5 ga watan Maris.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wadanda abun ya ritsa da su dukkaninsu maza sun kasance yan gida daya ne, kuma cikinsu akwai magidanta.
Yadda hatsarin ya afku tsakanin Gulf da motar kaya
An tattaro cewa motocin sun yi tawo mu gama da wata motar daukar kaya da ke dauke da itattuwa wanda ya yi sanadiyar mutuwarsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani mazaunin garin Kachia wanda ya san wasu daga cikin mutanen da abun ya ritsa da su, Isiyaku Musa Kachia ya fada ma Daily Trust cewa dukkaninsu yan Kano ne amma suna zaune a garin Kachia ta jihar Kaduna.
Ya ce:
"Na san yawancinsu. Sun je mahaifarsu a Kano don halartan bikin aure amma a hanyarsu ta dawowa garin Kachia sai motar da suke tafiya da ita ta yi tawo mu gama da wata motar daukar kaya da ke dauke da itattuwa, kuma dukkansu sun mutu a nan take."
A cewarsa, an binne su a ranar Litinin, 6 ga watan Maris a Kachia daidai da koyarwar addinin Musulunci.
Kwamandan hukumar hana afkuwar hatsarurruka na FRSC, Zubairu Mato ya tabbatar da lamarin, inda ya danganta shi da kokarin shan gaban wata mota wanda ya sa motar ya kwacewa direban.
A cewarsa, motar kirar Gulf ya dauki abun da ya fi karfinsa a daidai lokacin da hatsarin ya afku. Ya ce daga cikin mutanen da suka mutu akwai manya 8 da yara biyu.
A wani labari na daban, zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu, ya ce dole a hada kai don magance matsalar tsaro a Najeriya.
Asali: Legit.ng