Buhari Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Abacha Kan Mutuwar Dansu

Buhari Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Abacha Kan Mutuwar Dansu

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa kan mutuwar dan marigayi shugaban kasa, Sani Abacha
  • Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga Hajiya Maryam Abacha kan mutuwar danta, Abdullagi Abacha
  • Marigayin ya amsa kira mahaliccinsa a cikin barcinsa kuma tuni aka yi jana'izarsa

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga matar tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Hajiya Maryam Sani Abacha, da ahlinta kan mutuwar dansu Abdullahi.

Shugaban kasar ya nuna alhininsa kan mutuwar a cikin wata sanarwa da mai bashi shawara a kan kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya saki a ranar Asabar, 4 ga watan Maris a Abuja, jaridar Premium Times ta rahoto.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaune
Buhari Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Abacha Kan Mutuwar Dansu Hoto: MBuhari
Asali: Twitter

A cewar hadimin shugaban kasar, addu'a da zuciyar shugaban kasar na tare da iyalan Abacha yayin da suke alhinin mutuwar matashi Abdullahi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hawaye, Alhini Yayin Da Dan Marigayi Sani Abacha Ya Rasu A Abuja

Shugaban kasar ya yi addu'an Allah ya ji kan mamacin sannan ya baiwa masu alhinin mutuwar juriyar wannan babban rashi da suka yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abdullahi ya rasu a cikin baccinsa

An tattaro cewa Abdullahi ya mutu ne a cikin baccinsa a ranar Asabar kamar yadda yayarsa kuma amaryar gwamnan jihar Yobe, Gumsu Sani Abacha.Mai Mala Buni ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a soshiyal midiya.

Ta wallafa a shafinta na Twitter:

"Innalillahi wa'inna illaihi raji'un. Na rasa kanina Abdullahi Sani Abacha. Ya mutu a cikin barcinsa. Allah Ubangiji ya yafe masa kura-kuransa sannan ya sada shi da jannatul firadous, Ameen. Dan Allah ku sanya shi a addu'o'inku."

An binne gawarsa a makabartar Gudu da ke Abuja bayan an sallace shi a babban masalacin Juma'a a Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan Amurka Da Birtaniya, Sarkin Wata Babban Kasa Ya Sake Taya Tinubu Murnar Cin Zaben Shugaban Kasa

Hakimin Basirka, Muhammad Suleiman, da yaransu 3 sun rasu a hadarin mota a Jigawa

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa dan Amar na masarautar Dutse kuma hakimin Basirka a Jihar Jigawa ya rasu tare da yaransa su uku.

Kamar yadda rahotanni suka kawo, basaraken ya rasu ne ta sanadiyar hatsarin mota a hanyarsa ta zuwa garin Gwaram tare da iyalansa.

Yaransa guda uku suma sun amsa kiran mahaliccinsu tare da shi yayin da matarsa da sauran yara biyu suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng