Adadin Kujerun Majalisan Da APC, PDP, NNPP, Da Sauran Jam'iyyu Suka Samu
- Kujeru a majalisar dattawan tarayya: APC 59, PDP 29, LP 6, NNPP 2, SDP 2, APGA 1, YPP 1
- Kujeru a majalisar wakilan tarayya: APC 262, PDP 102; LP 34; APGA 4; ADC 2, SDP 2, YPP 1
- Adadin kujerun da aka kammala zabe a kansu kawo yanzu sune; 98 na majalisar dattawa, 325 na majalisar wakilai
Hukumar shirya zaben ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta bayyana cewa sabuwar majalisa ta 10 da za'ayi itace ta farko irinta a tarihin Najeriya tun 1999 da aka dawo siyasar demokradiyya a Najeriya.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ranar Asabar a zamansa da kwamishanonin INEC (RECs) a hedkwatar hukumar dake Abuja.
Ya ce a zaben da ya gabata, an kammala zaben mazabun majalisa 423 yayinda za'a yi karashen zabe a mazabu 46.
Ya bayyana cewa a majalisar dattawa, zabe ya kammala a mazabu 98 cikin 109 kuma jam'iyyu bakwai suka samu wakilai.
Yayinda a majalisar wakilai an kammala zabe a mazabu 325 cikin 360 kuma jam'iyyu takwas ne suka raba kujerun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A majalisar dattawa, jam'iyyar All Progressives Congress APC ta samu kujeru 57; jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta samu 29; jam'iyyar Labour Party LP ta samu 6; jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ta samu biyu, hakazalika Social Democratic Party (SDP).
Sannan jam'iyyar Young Peoples Party (YPP) da All Progressives Grand Alliance (APGA) da suka samu kujera 1.
A majalisar wakilai kuwa, APC ta samu kujeru 262, PDP 102; LP 34; APGA 4; ADC 2, SDP 2, sannan YPP 1.
Gwamnoni biyu sun yi nasara
Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya samu nasarar lashe zaɓen sa domin wakiltar Ebonyi ta Kudu a majalisar dattawa.
Umahi, wanda shine ɗan takarar jam'iyyar APC, ya samu ƙuri'u 28,378, inda ya doke ɗan takarar Labour Party, Linus Okorie, wanda ya samu ƙuri'u 25,496
Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya samu nasarar lashe zaɓen sanatan Neja ta Arewa a ƙarƙashin inuwar APC.
Gwamna Bello, ya samun nasara bayan ya samu ƙuri'u masu rinjaye a zaɓen inda ya samu ƙuri'u 100,197, domin kayar da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Shehu Muhammad Abdullahi, wanda ya samu ƙuri'u 88,153.
Asali: Legit.ng