Taron Majalisar Ɗinkin Duniya: Buhari Ya Shilla Gamida Keta Hazo A Jirgin Sama Zuwa Doha
- Tafiyar Zuwa Birnin Qatar Ta biyo Bayan Gayyatar Da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani Yayi Wa shugaba Buhari ne Domin Halartar.
- Ana Yin Taron ne Domin Samun Taimakon Ƙasashen Duniya Wajen Samun Tabbattaccen Cigaba Mai Ɗorewa.
- Shugaba Muhammadu Buhari yayi alƙawarin Faɗawa mahalarta taron Yadda Najeriya Take taimakawa ƙasashe marasa galihu samun cigaba mai ɗorewa.
A karon farko tun bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisu tare da faɗin sakamakon zaɓen.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya shilla zuwa wani taron Majalisar Dinkin Duniya akan ƙasashe masu tasowa na 5 dazai gudana a Doha, babban birnin ƙasar Qatar.
A wani saƙo da Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ƙasa na musamman ya gabatar, ya tabbatar wannan batu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hukuncin da Kotun ƙoli ta Yanke Na Canjin Fasalin Kuɗi Zai Kasance Kyakkyawan Tushe Ga Mulkin Tinubu — Yahaya Bello
Sakon na Garba Shehu ya tabbatar da cewa tafiyar ta Buhari nada alaƙa da gayyatar da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani yayi wa shugaba Buhari.
Shi dai taron ana fatan yin sa daga 5 ga watan Maris ne zuwa 9 ga watan Maris 2023.
Taron mai taken "Daga Alamun Cigaba Zuwa Cigaban Ƙasashe" yana faruwa ne sau ɗaya a cikin shekaru guda goma.
Ana yin taron ne domin domin neman taimakon ƙasashen duniya wajen samun tabbattaccen cigaba mai ɗorewa.
Bayanin na Garba Shehu yace:
"A Doha, shugaba Muhammadu Buhari zai yi ƙoƙarin tabbatarwa ƙasashen duniya akan jajircewar Najeriya wajen taimakawa ƙasashe marasa galihu samun cigaba mai ɗorewa, ta hanyar nunawa duniya hanyoyi daban daban da Najeriya tayi amfani dasu a lokuta da dama.
"Ƙasashen nan marasa galihu suna samun tasgaro wajen samun yadda zasu warware matsalolin su dake hana su samun cigaba mai ɗorewa, da suka haɗa da, talauci, canjin yanayi abinci da kuma matsalar makamashi gamida bashi da yayi musu katutu."
Bayanin da jaridar The Nation ta ruwaito ƙarƙare da:
"Shugaban na Najeriya zai tabbatar da ya nuna muhimmancin samun amsoshi da zasu warware matsalar dake fuskantar ƙasashe da suke hana su samun cigaba mai ɗaurewa"
Gwamna Wike Ya Yaba da Hukuncin Kotun Koli Kan Sauya Fasalin Naira
Yanayin bazata yasa Nyesom Wike na jihar Ribas, a ranar Jumu'a, ya goyi bayan hukuncin Kotun ƙoli wanda ya tsawaita wa'adin amfani da tsohon naira N200, N500 da N1000 zuwa 31 ga watan Disamba.
Wike ya ɗaure gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, inda ya ce ba shi da wani zaɓi illa yin biyayya ga umarnin Kotun daga ke sai Allah ya isa.
Gwamna Wike ya yi wannan jawabin ne lokacin da yake kaddamar da wasu muhimman ayyuka a jihar Oyo jim kaɗan bayan Kotun koli ta yanke hukuncin karshe ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng