Zaɓukan 2023: INEC na Barazanar Soke Zaɓukan Jihar Kogi.

Zaɓukan 2023: INEC na Barazanar Soke Zaɓukan Jihar Kogi.

  • Kwamishinan Zaɓen na Jihar Gogi Yace Tabbas Da Yiwuwar Su Soke Zaɓukan Kogi Duba Da Irin Sa-toka-Sa-Katsin Daya Afku A Jihar
  • Mopa Dake Kogi Ta Yamma Da Kuma Wasu Sassa Na Kogi Ta Tsakiya An Samu Rikita-Rikitar
  • Za'a Jira Har Sai Sakamakon Zaɓen Ya Gama Zuwa Sannan A Yanke Hukunci Kafin daga Bisani A Fitar Da Matsaya

A jiya ne yan Najeriya suka kada kuriun su a zabukan dake gudanar yanzu haka a kasar. Zaben wanda yazo da matsaltsalu da suka hada da sace akwatunan zabe, kaiwa ofishisoshin yan sanda hari tare da rashin fitowar masu aiki da kuma masu zabe a wasu wurare da dama na kasar.

Jihar Kogi ma ba'a barta a baya ba wajen fuskantar wannan kalubale kamar ko wacce jiha. Rahotanni na nuna cewar, hukumar zaɓe ta ƙasa ka iya rushe gamida ƙin amfani da sakamakon zaɓen jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Faɗa Ya Kaure Tsakanin Magoya Bayan NNPP da APC a Jihar Kano

Hakan na zuwa ne yayin da da aka kammala kada ƙuriu a mafi yawa daga lungu da saƙo na ƙasar nan a zaben da akai Asabar ɗin data gabata na Shugaban Ƙasa da ƴan majalisar dattawa da wakilai.

Inecboss
Zaɓukan 2023: INEC na Barazanar Soke Zaɓukan Jihar Kogi. Hoto: Gurdianng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, hukumar INEC tayi barazanar soke zaɓen ne sakamakon tashe -tashen hankula da aka samu yayin gudanar da zaɓukan a Kogi.

Dr Hale Longpet, shine Kwamishinan Zaɓe na jihar Kogi. Kuma shine ya tura saƙon yiwuwar hakan lokacin da yake maida martani abisa rigimar data ɓarke a wasu ƙananan hukumomi na jihar.

Tunda fari dai, an samu rahotannin wasu yan jagaliyar siyasa ne da suka shiga guraren akwatunan zaɓe a Anyigba da Dekina dake gabashin Kogi suka aikata ta'annati.

Sannan a Mopa dake Kogi ta yamma da kuma wasu sassa na Kogi ta tsakiya an samu makamancin irin wannan balahirar yayin da wasu ɓata gari sukayi awon gaba da akwatunan zaɓe zuwa wuraren da ba'a sani ba.

Kara karanta wannan

Yadda Masu Kada Kuri'a Sukayi Karanci Basu Fito ba a Kaduna Ya Dame Ni - El-Rufai.

Wannan dalili ne yasa hankalin Kwamishinan zaben yayi matukar kaduwa, inda yake cewa:

"Sanin kanku ne dai dokar zaɓe ta tanadi cewar, duk wani abu da aka samu ya hana zaɓe gudana, tabbas dole ayi fatali da sakamakon zaɓen; akwatun da duk wani abu na wajen.
" Lamarin ya faro ne daga Kogi ta Gabas da Kogi ta tsakiya, amma ina mai tabbatar muku cewa, bansan ina da ina bane aka samu irin wannan matsala ba saboda yawan su, zamu dai jira har sai sakamakon zaɓen ya gama zuwa sannan mu yanke hukunci."

Kwamishinan zaɓen ya kuma tabbatar ma majiyar mu cewar, wannan matakin da ƴan jagaliyar siyasa suka aikata a wuraren yasa masu kaɗa kuri'a da yawa basu samu damar kaɗawa ba.

Ya kuma bayyana mamakin sa akan yadda mutane suke amfani da wata dama wajen lalata abinda mutane da yawa zasu amfana dashi.

Longopet ya nuna damuwar akan yadda rikicin ya lamushe rayuka lokacin da aka jiyo shi yana cewa:

Kara karanta wannan

Tabbas Ina da Ƙwarin Gwuiwa Cewar Nine Zan Lashe Zaɓen Nan - Tinubu

"Wannan lamari ne mai matuƙar dugunzumarwa, musamman idan akayi duba da yadda lamarin ya ɗauki rayuka".

Inda yace zaɓe ba yaƙi bane, sannan ya kara jaddada nasiha ga masu neman mulki akan cewar:

"Inda har ka tsaya takara domin bautawa jama'ar kane, ba buƙatar ka shiga harƙallar da zata saka ka lalata dukiya da rayukan su", inji shi.

Daga ƙarshe kuma Kwamishinam zaɓen na Kogi ya nuna kin dadin sa akan yadda cikin Lokoja ya kasance da salama yayin gudanar da zaɓen.

A cewar sa, ko murya basa ɗagawa saboda tsari da son zaman lafiya.

A wani labarin daban kuma wasu mata ne suka rasa rayukan su a zabben dake gudana a jihar Bayelsa.

An Bindige Mata Biyu a Bayelsa Yayin da Rikicin Zabe Ya Kaure a Ribas

A cikin ire iren kalubalen da ake samu a zabukan kasar nan. Legit Hausa ta ruwaito yadda wasu bata gari suka harbi mata biyu yayin zaben shugaban kasa a gudunmar Ofoni ta jihar Bayelsa.

Jaridar taruwaito cewar dandazon masu zabe ne bayan harbin suka cafke biyu daga cikin matasan da suka yi harbin nan inda take suka mika su ga yan sanda A jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida