Ina Kyautata Zaton Ni Zan Lashe Zaben Nan: Atiku Yayinda Ya Kada Kuri'arsa

Ina Kyautata Zaton Ni Zan Lashe Zaben Nan: Atiku Yayinda Ya Kada Kuri'arsa

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kada kuri'arsa a zaben dake gudana yau
  • Atiku na cikin daya daga cikin manyan yan takara hudu dake fafatawa a zaben INEC 2023
  • INEC ta bayyana cewa karfe 2:30 za'a rufe ka'da kuri'u sannan a fara kirgan kuri'u

Jimeta - Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya kada kuri'arsa a mazabarsa dake jihar Adamawa.

Atiku ya bayyanawa manema labarai cewa yana kyautata zaton cewa shine zai yi nasara a zaben, rahoton Vanguard.

Atiku
Atiku Yayinda Ya Kada Kuri'arsa Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya ce ya kada kuri'arsa cikin sauki kuma yana sa ran haka kowa zai ka'da nasa ba tare da wahala ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Zabe Ya Gabato, Har Yanzu Babban Ministan Buhari Ya Ki Yarda Ya Goyi Bayan Tinubu

A cewarsa:

"Ina kyautata zaton yin nasara."

Dan takara da kansa a jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa kowa ya fita ya kada nasa.

A cewarsa:

"Yanzu na kada kuri'ata. Kowa ya taka nashi rawar ganin domin gayara ranar goben kasar mu."

'Rana bata karya'

Allah ya kawo mu ranar zaben shugaban kasar Najeriya 2023 inda yan Najeriya ke zaben wanda zai ja ragamar mulkin kasar daga 2023 zuwa 2027.

Yan takara 18 ne zasu fafata a wannan zabe kuma mutum milyan 87 da suka karbi katunan zabensu ake sa ran zasu fito ka'da kuria, bisa alkaluman INEC.

Yan takaran sun hada da:

1. Christopher Imumolen – Accord Party (AP)

2. Hamza Al-Mustapha – Action Alliance (AA)

3. Omoyeole Sowore – African Action Congress (AAC)

4. Dumebi Kachikwu – African Democratic Congress (ADC)

5. Yabagi Yusuf Sani – Action Democratic Party (ADP)

Kara karanta wannan

2023: Abubuwa 10 da baku sani ba game da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a PDP

6. Ahmed Bola Tinubu– All Progressives Congress (APC)

7. Umeadi Peter Nnanna – All Progressives Grand Alliance (APGA)

8. Ojei Princess Chichi – Allied People’s Movement (APM)

9. Nnamdi Charles Osita – Action Peoples Party (APP)

10. Adenuga Sunday Oluwafemi – Boot Party (BP)

11. Obi Peter Gregory – Labour Party (LP)

12. Musa Rabiu Kwankwaso – New Nigeria Peoples Party (NNPP)

13. Osakwe Felix Johnson – National Rescue Movement (NRM)

14. Abubakar Atiku – Peoples Democratic Party (PDP)

15. Abiola Latifu Kolawole – Peoples Redemption Party (PRP)

16. Adebayo Adewole Ebenezer – Social Democratic Party (SDP)

17. Ado-Ibrahim Abdumalik – Young Progressives Party (YPP)

18. Nwanyanwu Daniel Daberechukwu – Zenith Labour Party (ZLP)

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida