An Damke N2m Na Dan Siyasa Za'a Sayi Kuri'u Da Su A Gombe

An Damke N2m Na Dan Siyasa Za'a Sayi Kuri'u Da Su A Gombe

  • Kuma dai, an damke wani mutumi dauke da tsabar kudi dake da tsada a wannan marrar
  • Wannan shine karo na uku da za'a kama wasu yan siyasa da makudan kudi ana shirin yin zabe
  • A jihar Legas, EFCC ta damke wani dan siyasa da kudi milyan talatin da biyu za'a sayi kuri'u da su

Bauchi - Jami'an rundunar 33 Artillery Brigade Operation Safe Conduct dake Alkaleri, jihar Bauchi sun damke wani mutumi dauke tsabar kudi Naira milyan biyu.

Mutumin mai suna Hassan Ahmed ya shiga hannun Sojin yayinda yake hanyar tafiya zuwa Gombe, rahoton ChannelsTV.

Sojojin sun damkeshi ranar Juma'a kuma suka damkashi hannun jami'an hukumar yaki da rashawa ICPC, shiyar jihar Bauchi.

Hassan
An Damke N2m Na Dan Siyasa Za'a Sayi Kuri'u Da Su A Gombe Hoto: channelstv
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ana Gobe Zabe, An Kama Wani Mutum Da Maƙuden Miliyoyin Naira A Mota Zai Kai Wa Ɗan Siyasa A Gombe

An damke Ahmad dauke da N900,000 na sabbin kudi, da kuma N1.1 million na tsaffin kudi cikin mota kirar Hilux mai lamba JMA 85 AZ.

An gano kudin cikin jaka “Ghana Must Go” dauke da bandirin sabbin duba daya-daya na N600,000; bandir shida na dari biyar na kudi N300,000 sannan yan dari biyu-biyu na tsaffin kudi N1.1 million.

ICPC tace mutumin ya bayyana cewa yana shirin kaiwa wani dan siyasa kudin ne a Gombe.

Hukumar EFCC Ta Cafke Maƙudan Kuɗaɗen Siyan Ƙuri'a a Zaɓen Shugaban Ƙasa

A wani labarin kuwa, Hukumar hana cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta samu nasarar cafke wasu maƙudan kuɗaɗe da aka yi niyyar siyan ƙuri'a da su a jihar Legas.

Hukumar ta EFCC ta cafke naira miliyan talatin da biyu da dubu ɗari huɗu waɗanda ake zargin za a yi amfani da su wajen siyan ƙuri'a a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Kamfen Kwankwaso: An kame 'yan daba 55, an kone wani adadi na motoci a Kano

Hukumar EFCC shiyyar jihar Legas ta sanar da cewa tuni aka tasa ƙeyar wanda ake zargin domin amsa tambayoyi.

Sai dai hukumar ba tayi ƙarin haske ba kan sunan wanda aka cafken da kuma wacce jam'iyya yake yiwa aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida