Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Orji Uzor Kalu, Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattijai
- Rikicin jam'iyyar APC a jihar Abia ya dau sabon salo ana kasa da kwana guda zaben shugaban kasa
- Babban jigon jam'iyyar APC a jihar ya shiga takun saka da shugabannin jam'iyyar a jihar
- Orji Kalu a yanzu haka dan takara ne a zaben Sanatoci da zai gudana gobe Asabar, 25 ga wata
Abia - Ana kasa da kwana daya zaben shugaban kasa da yan majalisar dokokin tarayya, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Abia ta dakatar da dan takararta a zaben Sanata mai wakilyar Abia ta Yamma, Orji Uzor Kalu.
Uzor Kalu tsohon gwamnan jihar Abia ne kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa a majalisar dattawa kuma mai tsawatarwa a majalisar.
Jam'iyyar ta sanar da dakatar da shi ne a takardar da shugaban kwamitin ladabtarwa, Barr Paul Nwabuisi, sakataren jam'iyyar, Cif Chidi Avaja, da shugaban jam'iya, Dr Kingsley Ononogbu, suka rattafa hannu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an dakatar da Uzor Kalu ne bisa yiwa jam'iyyar zagon kasa a jihar.
Wani sashen takardan yace:
"An dakatar da shi ne bayan bincike mai zurfi da shawarin kwamitin ladabtarwa da gundumar Igbere, karamar hukumar Bende da kuma shugabannin jam'iyyar."
"Ku sani cewa jam'iyyar ta damu da mutuncinta saboda haka ba zata lamunci wani zagon kasa ba."
"Bayan samun isassun hujjojin dakatar da kai, wajibi ne mu kare mutuncin jam'iyyarmu."
An tattaro cewa rikici da ya barke a jam'iyyar APC ta jihar Abia ya ta'azzara ne biyo bayan hirar da Sanata Uzor Kalu yayi inda yace ba zai goyi bayan dan takarar gwamnan jihar na APC ba.
Ya ce ta wani dalili zai goyi bayan wani alhalin dan'uwansa kuma jininsa na takara a wata jam'iyyar.
Yanzu-Yanzu: Hoto, Bayanai Sun Fito Yayin Da Yan Sanda Suka Kama Sanannen Dan Majalisar Wakilai Da Dala 498,000 Cikin Jaka
Sanatan APC Ya Bayyana Abinda Inyamurai Zasu Yi Domin Samun Mulkin Najeriya
A wani labarin kuwa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa ƴan Najeriya basu shirya samun Inyamuri a matsayin shugaban ƙasa ba.
Uzor Orji Kalu ya bayyana hakan ne a yayin wata tattauna da gidan talabijin Channela a shirin su mai suna "The 2023 Verdict" a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng