Fusatattun Matasa Sun Kaiwa Gwamna Zulum Hari a Jihar Borno
- Gwamnan Borno ya shiga jerin yan takaran da aka kaiwa hari ana shirye-shiryen zaben 2023
- Ana saura kwana daya zabe wasu matasa sun kaiwa gwamnan jihar Borno hari a cikin Maiduguri
- Yan siyasa na komai kananan hukumominsu domin kada kuri'unsu ranar Asabar
Borno - Wasu fusatattun matasa sun kaiwa tawagar motocin gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a birnin Maiduguri.
ZagaZola Makama ya ruwaito cewa wannan ya auku ne da yammacin Alhamis, 23 ga watan Febrairu, 2023.
Rahoton yace gwamnan na hanyar dawowarsa dake mahaifarsa Mafa lokacin da matasan su far musu.
Rahoton da ZagaZola ya wallafa a Tuwita, ya bayyana cewa irin haka aka kawai matar gwamnan hari yan kwanaki da suka gabata a Konduga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yace:
"Da yammacin 23 ga Febrairu, wasu matasan unguwar Kaleri dake Maiduguri sun kaiwa tawagar motocin gwamna Borno, Babagana Zulum, hari yayinda yake dawowa daga Mafa, mahaifarsa, inda aka lalata motocinsa uku."
"Majiyoyi sun bayyana cewa motocin da aka lalata sun hada na yan jarida, injiniyoyi da wata mota guda."
Rahoton ya kara da cewa kwanakin baya matasa irin haka sun kaiwa uwargidar gwamnan, Hajiya Falmata Zulum, hari a Dalori, karamar hukumar Konduga.
An lalata motoci 8.
Yan Bindiga Sun Kara Kai Mummunan Hari a ofishin Yan Sanda a Abia.
A wani labarin daban, wasu ƴan bindiga da za'a iya kira da ƴan bindiga-daɗi suka ƙaddamar da wani mummunan hari a wani ofishin ƴan sanda dake yankin Ugwunagbo ta jihar Abia.
Lamarin na zuwa ne, ƙasa da awanni arba'in da takwas domin gudanar da zaɓukan ƙasar.
An ruwaito cewar, lamarin ya faru ne a yayin da wasu yan sanda guda biyu suke tsaka da aikin su, kafin daga bisani maharan suzo musu da wani salo irin samfurin kwantan ɓauna.
Zuwan su keda wuya, sai suka soma aman wuta kota ina batare da ƙaƙƙautawa ba. Hakan yasa ƴan bindigan suka fi ƙarfin yandan guda biyu, wanda saboda haka ne suka cinnawa ofishin wuta nan take.
Babban ɗan sandan yankin da aka fi sani da DPO ya tsallake rijiya da baya, domin rahoton da Jaridar The Nation ta saki, ya nuna DPO ɗin aka so a kashe.
Asali: Legit.ng