Zaben 2023: Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Bada Umurnin Rufe Dukkan Iyakokin Kasa
- Hukumar shige da fice ta Najeriya ta sanar da kulle iyakokin kasar nan tsawon awa ashirin hudu a cigaba da shirin babban zabe
- Shi ma shugaban yan sandan Najeriya ya bada umarnin sanya dokar takaita zirga-zirga a fadin kasar a lokacin zabe
- Hukumomi a Najeriya sun fara sanya dokoki na musamman a cigaba da shirye-shiryen babban zaben na 2023
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta umarci a rufe iyakokin kasar nan a shirye-shiryen babban zabe, kamar yadda ta sanar a shafinta na Twitter.
Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya ne a ranar 25 ga Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis Tony Akuneme, mai magana da yawun hukumar shige da fice na Najeriya, Isah Jere, shugaban hukumar shige da fice, ya ce za a kulle iyakokin tsahon awa 24 a ranar zaben.
Rufe iyakar zai fara ne daga 12 na daren Asabar zuwa 12 na daren ranar Lahadi.
''Saboda haka, kwamandoji musamman da ke kan iyakokin kasa da su tabbatar da an bi dokar yadda ya kamata,'' a cewar sa.
Hakan na zuwa ne awanni kadan bayan Usman Alkali Baba, shugaban yan sandan Najeriya, ya sanya dokar takaita zirga-zirga a fadin kasar ranar zabe.
Dokar, wanda ta ware masu ayyuka na musamman, za ta fara aiki daga tsakar daren Juma'a zuwa 6 na yammacin Asabar 25 g watan Fabrairu da ake fatan yin zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi magana kan zaben Najeriya, ya mika sako ga yan kasa da yan siyasa
A wani rahoton kuma sun ji cewa kasar Amurka ta yi kira ga al'ummar Najeriya su fita kwansu da kwarkwata cikin lumana su zabi shugabannin da za su musu jagoranci a kasar.
Joe Biden, shugaban na Amurka cikin wani sako da ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fayyace cewa kasarsa ba ta da wani dan takara da ta ke marawa baya, sai dai tana goyon bayan zabe na adalci mai nagarta.
Biden ya kuma jinjinawa yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyun siyasa a kasar da suka halarci taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, yana mai cewa hakan ya nuna sun yarda da zaben lumana.
Asali: Legit.ng