'Yan Bindiga Sun Halaka Dan Takarar Sanata da Wasu Mutane 5 a Enugu

'Yan Bindiga Sun Halaka Dan Takarar Sanata da Wasu Mutane 5 a Enugu

  • Yayin da ya rage awanni babban zabe, wasu yan bindiga sun kashe ɗan takarar Sanata a jihar Enugu da yammacin Laraba
  • Mista Oyibo Chukwu ya rasa rayuwarsa tare da wasu magoya baya 5 a hannun maharan waɗanda suka cinna wa motarsu wuta
  • Ɗan takarar gwamna a LP ya ce a yanzun mambobin jam'iyyar rayuwarsu na cikin haɗari kullum sune abun hari

Enugu - Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun halaka tare da ƙona ɗan takarar Sanatan jam'iyyar Labour Party a mazaɓar Enugu ta gabas, Mista Oyibo Chukwu.

Tsagerun 'yan ta'addan sun kashe magoya bayansa mutum 5 wadanda ke tare da ɗan siyasan a cikin motarsa.

Mr Oyibo Chukwu.
'Yan Bindiga Sun Halaka Dan Takarar Sanatan LP, Mista Oyibo Chukwu. Hoto: vanguard
Asali: UGC

Jaridar Punch ta tattaro cewa mummunan lamarin ya auku ne a Amechi Awkunanaw da ke yankin ƙaramar hukumar Enugu ta kudu da yammacin ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban PDP da Jagoran Al'umma a Kaduna

Mai neman zama gwamnan Enugu a inuwar Labour Party a zabe mai zuwa, Chijioke Edeoga, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce yan bindigan sun harbe ɗan takarar Sanatan da sauran mutane 5 da suka tare a cikin motarsa sannan suka banka musu wuta.

"Eh dagaske ne ɗan takarar Sanatan mu a mazaɓar Enugu ta gabas a zaben ranar Asabar mai zuwa ya rasa rayuwarsa. Sun (yan bindiga) kashe shi da wasu mutane 5 a cikin mota kana suka cinna masu wuta."
"Rayukan mambobin jam'iyyar mu suna cikin haɗari, a ko da yaushe nemansu ake da kisan kai, muna zargin jam'iyyun siyasa waɗanda ke ganin LP ta zame masu barazana a jihar nan."

"Kuma jam'iyyun suna fargabar zasu iya shan kaye a zaben ranar Asabar (25 ga watan Fabrairu, 2023)," inji shi.

Kara karanta wannan

Zafafan Hotunan Kamfen Tinubu/Shettima Na Karshe Da Ya Gudana a Legas

Idan zaku iya tunawa, mahara sun kai hare-hare wurin tarun kamfen LP da wasu harkokin siyasar jam'iyar, sun jikkata mambobi kuma sun lalata kadarorin miliyoyin kudi.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin rundunar yan sandan Enugu ya ci tura domin ba'a samu jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, DSP Daniel Ndukwe, ba lokacin da aka tuntuɓe shi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yan bindiga sun sace manyan mutane 2 a Kaduna

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban PDP da Jagoran Al'umma a Kaduna

Mahara sun shiga yankin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna, sun yi awon gaba da shugaban PDP na gundumar Dan Mahawayi, Alhaji Bala Alhassan Marafa.

Mazauna kauyen sun ce wannan shi ne karon farko da yan bindiga suka aikata haka a garin duk da suna zuwa biyan buƙata da shan shayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262