Abinda Yasa Har Yanzu Bamu Kama Kowa Kan Karancin Naira Ba, EFCC
- Shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumarsa ta ɗan jira ne don kar ta ƙara dagula tsarin sauya naira
- An yi tsammanin EFCC zata sa ido kan masu maida tsohon kuɗi bankuna domin cafke masu boye dammai a gida
- Bawa ya ce sabbin naira suna da lambobin da za'a iya gano daga inda suka fito kuma me aka yi da su
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa (EFCC) ta ce ba ta maida hankali wajen kama waɗanda ake zargin suna ɓoye takardun kuɗi a gida ba duk da karancin sabbin kuɗin.
Shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa, ne ya bayyana haka yayin hira da Channels tv cikin shirinsu mai taken, The 2023 Verdict, ranar Laraba.
"Ina tunanin wasu ma'aikata ko yan kasuwa da ake tantama game da halayensu suna nan da kuɗin sun tara," inji Bawa.
Ya kuma jaddada cewa doka ta baiwa kowane ɗan Najeriya dake tattare da tsoffin takardun naira ya maida su babban bankin Najeriya (CBN) a duk lokacin da ya so.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Tun farkon fara sabon tsarin daga watan Oktoba, 2022 zuwa yau bamu kama kowa ba. Ba mu ɗaga yatsa game da wanda ya maida kudi, inda ya kai kuma nawa ne ba saboda bamu son gurbata tsarin."
"Ɗaya daga cikin manyam manufar bullo da tsarin shi ne a tabbatar da dukkan takardun kuɗi sun koma hannun bankuna, shiyasa muka jinkirta, ba mu son fara kame."
- Abdulrasheed Bawa.
Mista Bawa ya ƙara da cewa sabbin takardun naira sun fi sauki wurin bin diddigi saboda lambobin sirrin da aka sanya masu da kuma wuraren da aka rarrabasu a ƙasar nan.
Ya ce hukumar EFCC ta samu karin nauyi na kwato dukkan kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayen kuri'un a lokacin babban zabe mai zuwa.
"Zamu iya bin kwakkwafi mu gano cewa shin kuɗin daga ATM aka ciro su ko kuwa wani can ya baiwa yan siyasa," inji shi.
Kwastomomi Sun Banka wa ATM Wuta a Jihar Legas
A wani labarin kuma Fusatattun mutane sun cinnawa ATM wuta jim kaɗan bayan kuɗin dake cikin sun kare a Legas.
Hukumar yan sanda ta bayyana yadda mutanen suka aikata amma jami'ai suka kai ɗauki a kan lokaci aka shawo kan lamarin cikin kankanin lokaci.
Asali: Legit.ng