"Kutse Aka Min A Facebook Da Instagram": Aisha Buhari Ta Kare Kanta Kan Wallafa Labarin Karya

"Kutse Aka Min A Facebook Da Instagram": Aisha Buhari Ta Kare Kanta Kan Wallafa Labarin Karya

  • Aisha Buhari ta ce ba ita da daura labarin boge kan dage wa'adin amfani da tsaffin Naira ba
  • Aisha ta ce akwai wasu yan kutse da suka lashi takobin bata mata suna ta shafukanta na soshiyar midiya
  • Uwargidar shugaban kasan ta yi kira ga jami'an tsaro su dau mataki na gaggawa kan wadannan mutane

Uwargidar shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, tace jawabin da aka gani ta daura a shafukanta na yanar gizo kan tsaffin takardun Naira aikin masu kutse ne.

A ranar Talata, Aisha Buhari ta fitar da jawabin cewa an dage wa'adin amfani da tsaffin takardun Naira da watanni 3.

Labarin ya yadu a kafafen ra'ayi da sada zumunta kuma gidajen jarida da dama sun wallafa.

Ba tare da bata lokaci ba bankin CBN ya fitar da jawabin karyata labarin Aisha Buhari.

Kara karanta wannan

Tsoffin Naira: CBN Ya Karyata Labarin da Aisha Buhari Ta Wallafa a Shafukan Sada Zumunta

Aisha Buhari
Aisha Buhari Ta Kare Kanta Kan Wallafa Labarin Karya Hoto: Aisha Muhammadu Buhari/CBN
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yanzu dai ta goge labarin daga shafukanta na Facebook da Instagram da aka daura da farko.

Bayan haka ta fitar da sabon jawabi a shafinta na Facebook inda ta nesanta kanta daga labarin.

Ta bayyana cewa wani mai kutse ne ke kokarin bata masa suna.

Tace:

"Na samu labarin cewa an daura wani labarin karya a shafi na soshiyal midiya, Instagram wanda ke hade da shafina na Facebook da safen nan. Tuni na yi umurnin a goge."
"Ko shakka babu wadannan yan kutsen suka goge hotuna na tun daga 2018 zuwa bara lokacin da na daura hoton hannuna da lallen Tinubu."
"Mai wannan abun dan kutse ne, wanda ke da niyyar cin mutunci na ta shafukana na soshiyal midiya."
"Ya zama wjaibi jami'an tsaro su binciko wadanda ke da hakkin kula da shafuka na kuma su dau mataki."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hadimar Aisha Buhari ta tafi kotu, ta ce matar Buhari ta ci zarafinta, a bata diyyar N100m

Karancin Naira: 'Yan kasuwa sun ci gaba da karbar tsoffin kudi taron APC na wata jiha

An yi shagali da tsaffin takardun Naira a wajen kamfen jam'iyyar APC da Bola Tinubu da aka yi yau a jihar Legas.

Masu sayar da kayayyaki a wajen taron sun yi biris da dokokin CBN inda suke karbar tsaffin kudade babu ruwansu.

Zaku tuna cewa gwamnoni sun yiwa al'ummarmu alkawarin cewa kada su damu, Tinubu na hawa mulki zai sauke dokar Emefiele.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida