Ayi Hakuri: Bidiyo Yadda Aka Kama Matashi Da Bandir-Bandir Na Kudin Bogi
- An kama wani mutum da sabbin bandir-bandir na kudi yan N500 na bogi a wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya
- Ba a yi cikakken bayani game da yadda mutumin ya samu kudin ba ko kuma abun da ya aikata da shi kafin a kama shi
- Yan sanda sun tabbatar da cewar an kama mutumin da ake zargin kuma yana tsare a hannunsu don gudanar da bincike
Wani mutumi da aka kama da bandir-bandir na jabun kudi yan N500 ya yadu a wani bidiyo da ya bayyana a soshiyal midiya.
An gano mutumin wanda nan take aka mika shi ga yan sanda yana kokarin bayani ka don kare kansa amma dai ya amsa laifinsa.
Lamarin ya haifar da zazzafan martani, wanda hakan ke kara tabbatar da yaduwar kudaden jabu a kasar Najeriya.
An Yi Dirama Yayin Da Wani Ya Taho Ofishin CBN Na Kano Dauke Na Tsaffin Kudi N50m Cikin Buhu, Bidiyon Ya Bazu
Jabun kudade
Babban bankin Najeriya (CBN) ya gabatar da sabbin kudaden naira daban -daban tsawon shekaru kuma kowanne da ingantattun tsaro da za su hana yin na boginsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A lokacin da aka gabatar da sabbin kudi Shugaban kasa Muhammadu Buhariu ya yi alkawarin cewa abubuwan da ke tattare da sabbin kudin naira za su hana yin na boginsu, jaridar Guardian ta rahoto.
A kodayaushe yan damfara kan yi kokarin kwaikwayon kudi sannan su yi amfani da su wajen yaudara da damfarar abokan kasuwanci da shi.
Jama'a sun yi martani
@EmirSirdam ya ce:
"Ban san ta yadda ake gane kudin bogi ba. Dan Allah ko wani zai iya yi mun bayani?"
@codedjeff ya yi martani:
"Kun tuna wannan dan layi mai ruwan silba a tsakiyan kudi? Wannan shine na CBN. Ba za su iya kwaikwayon wannan ba."
CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya
@AniagoM ta ce:
"Wakilan siyada da za su raba wannan kudin sune mutanen da nake tausayawa, idan mutane suka gano cewa kudin bogi ne."
A ci gaba da gashi: El-Rufai ya yi umurnin ci gaba da karbar tsoffin kudi a Kaduna
A wani labarin, gwamnan Kaduna, Nasir El-rufai ya umurci ma'aikatu da hukumomin gwamnatin jihar da su ci gaba da karbar tsoffin kudi kamar yadda kotun koli ta bayar da umurni a hukuncin wucin gadi da ta saki.
Asali: Legit.ng