Karancin Naira: Gwamna Obaseki Ya Taimakawa 'Yan Jiharsa, Ya Kawo Bas Din Kyauta
- A ranar Laraba, fusatattun matasa sun yi zanga-zanga a Edo kan karar da gwamnatin jihar ta shigar a Abuja, tana nuna goyon bayan manufar CBN na sauya kudi
- A ranar Alhamis, mazauna Edo sun murmusa yayin da gwamnansu ya samar da hanyar saukaka masu kan halin da suke ciki na karancin naira a jihar
- Da suke martani, wasu yan Najeriya sun bayyana cewa wannan ci gaba ne mai a irin wannan lokaci da ake ciki, yayin da wasu suka ce ya yi latti
Edo - A karshe gwamnan jihar Edo ya amsa koken mutanensa yayin da ake ci gaba da fadi tashi a kasar saboda rashin wadatattun sabbin naira.
A kokarinsa na saukakawa al'ummar jiharsa halin da suke ciki na rashin kudi, Gwamna Godwin Obaseki ya samar da motocin bas na kyauta don jigilar mazauna jihar.
CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya
Obaseki ya tuna da yan Edo yayin da ake fama da karancin kudi
Obaseki ya bayyana hakan ne ta wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairun 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar ta ce:
"Bas din kyauta a ECTS don saukaka wahalar rashin tsabar kudi
"Na yi umurnin cewa daga yau Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, gaba daya motocin bas na Edo City Transport Service (ECTS) su dunga daukar fasinjoji kyauta a matsayin hanyar rage radadin da mutane ke fuskanta na rashin tsabar kudi.
"Wannan umurnin ya shafi dukkan hanyoyi kuma zai ci gaba da aiki har zuwa ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu, 2023, inda za a yi sanarwa na gaba kan lamarin.
"Gwamnatin ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kwantar da hankali da bin doka ya kuma tabbatar da cewar za a dawo da zaman lafiya nan ba da jimawa ba."
Jama'a sun yi martani
greatuyi ya yi martani:
"Allah ya yi maka albarka yallabai..Amma Yallabai, ya maganar abincin kyauta?"
sir_senrio ya rubuta:
"Bayan mutuwar mutane, ina ganin abun ya zo a kure yallabai."
needsesan ya ce:
"Zabe ya kusa...duk kun zata mutane mahaukata ne.
Kada ku yi tashe-tashen hankula, ku ku dau mataki ran zabe - Kwankwaso ga yan Najeriya
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Bola Tinubu, ya bukaci yan Najeriya da su guji tashe-tashen hankali saboda rashin tsabar naira.
Asali: Legit.ng