Bafade Mafi Tsufa a Masarautar Alaafin Na Oyo, Baba Keji Ya Kwanta Dama
- Rahoton da muka samo daga majiya ya bayyana cewa, Allah ya yiwa wani fitaccen Bafade a masarautar Alaafin na Oyo rasuwa
- Allah ya dauke Morenikeji Lasisi bayan shafe shekaru 120 a duniya, ya shafe shekaru 77 yana bauta a fadar Alaafin
- Rahoto ya bayyana kadan daga tarihinsa da kuma tasirinsa a masarautar ta Alaafin da ke Oyo a Kudu maso Yammacin Najeriya
Jihar Oyo - Morenikeji Lasisi, Bafade mafi tsufa a cikin fadawan Alaafin na Oyo wanda aka fi sani da ‘Baba Keji’ ya kwanta dama.
Rahoton Vanguard ya bayyana cewa, Lasisi ya rasu yana da shekaru 120 a duniya, kuma ya yi bauta a fadar Alaafin na tsawon shekaru 77, inda ya kwanta dama ranar Litinin 13 Faburairu, 2023 a fadar ta Oyo.
Sai dai, wata tattaunawa da jaridar The Guardian ta yi da Baba Keji ta nuna cewa, shi kansa bai san adadin shekarunsa, kawai dai ya yi kirdadon lokacin da yake da wayau ne.
Rasuwarsa na zuwa ne watanni 10 kacal bayan rasuwar Oba Lamidi Adeyemi III, wanda ya yi mulki a fadar na tsawon shekaru 51.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanene Baba Keji da kuma tasirinsa a masarautar Alaafin na Oyo
Ana yiwa Baba Keji kallon Bafade dan amana kuma mai juriya da aiki tukuru ga masarautar Alaafin na Oyo.
A cewar wasu daga cikin fadawan:
“Yana yin aikin da aka saka shi, ba gajiyawa, kamar yadda Alaafin ya umarta.”
Ya kuma yi shuhura a matsayin abokin tafiyar Alaafin a cikin fadar, wanda kuma aka ce ya tattara tarin sani game da tarihin baya na masarautar da tsatsonta.
Hakazalika, ana yiwa Baba Keji kallon wata taska ta ilimin masarautar Oyo mai dimbin tarihi.
Allah ya yiwa Alaafin na Oyo rasuwa
A wani labarin na baya, kunji yadda duniya ta kadu da samun labarin rasuwar Alaafin na jihar Oyo bayan shafe shekaru yana mulki.
An ruwaito cewa, fitaccen basaraken ya rasu ne a ranar 23 ga watan Afrilu, kuma nan take aka fara shirin jana'izarsa.
Oba Lamidi Adeyemi III, ya rayu shekaru 81 a duniya, ya shafe shekaru sama da 51 yana mulki a masarautar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
Asali: Legit.ng