An Gurfanar da Mutum 2 Gaban Kotu Kan Lakadawa Basarake Mugun Duka

An Gurfanar da Mutum 2 Gaban Kotu Kan Lakadawa Basarake Mugun Duka

  • Wasu maza biyu, Azeez Bashiru mai shekaru 41 da Sikiru Ogunrin sun gurfana gaban kotun majistare ta Iyaganku cikin Ibadan, da ke Oyo
  • An zargi wadanda aka gurfanar da cin zarafi da barazana ga rayuwar Sarki Akeem Tijjani, Baalen Igunrin gami da yunkurin tada tarzoma
  • 'Dan sanda mai gurfanar wa ya bayyana yadda biyun tare da wasu suka lakada wa sarkin suka da misalin karfe 4:00 na yamma ranar 22, ga watan Nuwamba, 2022 a titin Iseyin da jihar

An gurfanar da wasu maza biyu, Azeez Bashiru mai shekaru 41 da Sikiru Ogunrin mai shekaru 40, ranar Alhamis kotun majistare ta Iyaganku cikin jihar Oyo, bisa zarginsu da cin zarafi gami da yin barazana ga rayuwar wani basarake, Sarki Akeem Tijjani, Baalen kauyen Igunrin.

Gudumar kotu
An Gurfanar da Mutum 2 Gaban Kotu Kan Lakadawa Basarake Mugun Duka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

'Yan sanda suna tuhumar wadanda ke kare kansu da almundahana, cin zarafi, barazana ga rai da kuma yunkurin tada tarzoma, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ku Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudadenku, Zamu Bi Umurnin Kotun Koli: Gwamnatin Tarayya

Mai gurfanarwa, ASP Sikiru Ibrahim, ya shaida wa kotu yadda masu kare kansu da wasu da dama a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2022, misalin karfe 4:00 na yamma a titin Ibadan, suka lakada wa sarkin duka, gami da yin barazanar cin zarafin iyalinsa.

A cewarsa, wadanda ake zargi sun tsara kansu da burin tada tarzoma ta hanyar toshe titi da duwatsu, kwalabai da sauran makamai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda ake zargi sun ki amsa laifukan da ake tuhumarsu, Daily Trust ta rahoto.

Alkali, Mrs T.B Oyekanmi ta amince da bada belin wadanda ke kare kansu kan N100,000 kowanne su da tsayayyu biyu kan kudi kamar haka, daga bisani ta dage sauraron karar zuwa 1 ga watan Maris.

Matar aure ta maka mijinta a kotu kan kaurace mata a shimfidar aure

A wani labari na daban, wata matar aure kuma 'yar kasuwa a Nyanya da ke Abuja ta maka mijinta a gaban kotu kan kaurace mata da yayi a shimfidar aure.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Sabon Rudani, Mambobin PDP 8,000 Sun Koma APC a Arewa

Ta sanar da alkali cewa, ba ya kula da ita da 'danta daya sannan ya kware a cin zarafinta tare da dukanta.

Ta roki kotu da ta raba aurensu da shi sannan ta bata damar rike danta inda zai dinga biyanta N50,000 a kowanne wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng