A Daure Duk Dan Kasuwar Da Ke Shigo Da Tufafi Daga Kasar Waje: Dangote

A Daure Duk Dan Kasuwar Da Ke Shigo Da Tufafi Daga Kasar Waje: Dangote

  • Aliko Dangote ya bayar da shawarar a daure masu dillancin kayan masaku daga ƙasashen waje hukuncin dauri mai karfi
  • Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta nuna darasi ga wadanda aka kama ta hanyar tabbatar da cewa ba'a basu zabin biyan tara ba
  • Yadudduka da kayan sawa da ake shigo da su daga waje sun mamaye kasuwannin cikin gida na Najeriya

Babban ɗan kasuwa Aliko Dangote ya jajirce wajen ganin cewa an farfaɗo da masana’antar saƙa a Najeriya.

Da yake jawabi a taron shekara-shekara karo na 50 (AGM) na kungiyar masana'antun Najeriya (MAN) ya yi kira da a ɗaure 'yan Najeriya masu shigo da kayan masaƙu daga ƙasashen waje.

A cewar attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, yana da muhimmanci majalisar dokokin ƙasar ta zartar da wata doka da za ta hukunta sayar da kaya kasar waje ta hanyar ɗaure masu laifi ba tare da zabin biyan tara ba.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Bankuna Sun Haɗe Kai, Sun Fitar da Sabuwar Sanarwa Ana Tsaka da Rashin Sabbin Kuɗi

Dangite
A Daure Duk Dan Kasuwar Da Ke Shigo Da Tufafi Daga Kasar Waje: Dangote Hoto: WEF
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana ci gaba da shigo da kayan sarrafa haɗa tufafi

A 2019, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dakatar da bada dala don sayen kowane nau'i na kayan saƙar tufafi, don farfaɗo da masana'antar.

Sai dai kuma hakan bai hana ‘yan Najeriya shigo da su daga waje ba, hasali ma abin ya karu.

BusinessDay ta ruwaito cewa Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta rubuta a cikin rahotonta na kasuwanci cewa kayan saƙar tufafi ya ƙaru da kashi 257.9 cikin dari a cikin watanni uku na farkon shekarar 2021 zuwa Naira biliyan 171.8 daga Naira biliyan 48 a shekarar 2020.

Dangote, a cikin laccarsa mai taken “Agenda Setting for Industrialing Nigeria in the Next years” ya ce:

“Ga masana’antar saƙar tufafi, na yi imanin ya kamata gwamnati ta tsara doka a Majalisar Dokoki ta ƙasa da za ta sa duk wanda ya sayar da kayan saƙar tufafi na ƙasashen ƙetare da aka haramta, dole ne ya fuskanci zaman gidan yari ba tare da ba shi zaɓin biyan tara ba. Don haka za a ɗaure shi ne kawai, ko da na shekara biyu ne kawai.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wike Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Koli, Ya Faɗi Matakin Da Zai Dauka Kan Sabbin Kuɗi

"Ainihin da ke faruwa a masana'antar saƙar tufafi ba tsadar wutar lantarki ba ne. Harkar saƙar tufafi ba za ta yiwu ba idan kuka ba su wuta mai rahusa amma ana ci gaba da fasa ƙwauri.
"Abin da ke faruwa shi ne, kamfanonin ƙasashen waje suna hankaɗo da kayayyakinsu Najeriya.
"Shi ya sa ba na son shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Lokacin da kuke shigo da kaya, kuna shigo da talauci ne tare da fitar da wadata da guraben aikin yi."

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa Dangote ya kuma ce ya kamata gwamnati ta yi amfani da karfin da ta tara domin aiwatar da dokar hana shigo da shinkafa a yunkurin kawo ƙarshen fasa-ƙwaurin da ake yi a Najeriya.

Dangote ya ƙara da cewa:

"Ƴan shekarun da suka gabata, masana'antun saƙar tufafi a da su ne suka fi yawan ma'aikata bayan gwamnatin tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Abubuwa Sun Ɗau Zafi, Shugaba Buhari Ya Kori Shugaban NSITF Daga Aiki Kan Abu 1 Tak

"Yau kuma za a iya tura mutane gidan yari a Indiya saboda suna sayar da kayan saƙa na kasashen waje a ko'ina. Haka kuma, idan aka hana wani abu a Amurka misali, babu yadda za a yi a saka shi don a sayar da shi a cikin shago.
“Amma abin da ke hana aiwatar da manufofin gwamnatin Najeriya shi ne rashin tsarin siyasa na ganin mun aiwatar da waɗannan manufofin ko da wane ne ransa zai ɓaci.
"Idan muna da yanayi mai wadata, rashin tsaro zai ragu."

Rabi'u ya zama mutum na biyu mafi arziki a Najeriya

A wani labarin kuma, Arewa ta samu sabon matsayi na biyu a jerin attajiran Najeriya, kuma shi ne Abdulsamad Rabi'u Rabi'u.

Rabiu shi ne ya doke, hamshakin attajiri Mike Adenuga, a matsayi na biyu bayan jarin da ya zuba ya ƙara masa kuɗaɗen shiga na N87bn cikin sa'o'i.

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

Aliko Dangote har yanzu dai yana matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kuɗi a Najeriya kuma shi ne ɗan Najeriya ɗaya tilo da aka bayyana a cikin manyan attajirai 400 na duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida