Kai Tsaye: Yadda Kamfen Tinubu/Shettima Ke Gudana Yau a Sakkwaton Shehu
Kwamitin kamfen takarar kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyyar All Progressives Congress APC ta shiga cibiyar daular Islamiyya, a yau Alhamis, 9 ga watan Febrairu, 2023.
Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari
"Tun daga filin jirgin sama zuwa fadar Sultan zuwa nan mutane na tsaye a rana suna daga mana hannu, Nagode mutan Sokoto
Na rako dan takara na jam'iyyar, Ahmed Bola Tinubu, zamu goyi bayanshi kuma da yardan Allah zamu samu nasara.
Wadanda basu samu damar zuwa ba su fadawa iyalansu cewa mun zabi Bola Tinubu ya zama shugaban kasar nan da yardan Allah."
Jawabin Tinubu
"Akwai bukatar share PDP daga doron kasar Sokoto.
Da sunan Allah Muna muku alkawatin ingantaccen Ilmi, noma, kasuwancin kwarai"
Kwamishanonin Tambuwal, ma'ajin PDP sun koma APC a filin kamfe
Wasu kwamishanonin gwamnatin PDP a jihar Sokoto sun sanar da sauya shekarsu zuwa jam'iyyar a filin kamfen yanzu haka.
Shugaban kwamitin kamfen APC, Simon Lalong, ya ce yanzu babu gwamnati a jihar Sokoto.
Shugaban uwar jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya tdannan kwamishanoni.
Sun hada da:arbi wa
Jarman Sokoto, Alhaji Umarun Kwabo
Alhaji Murtala Dan Iya
Kwamishanan kanana hukumomi Haruna
Masu baiwa gwamna Tambuwal shawara 167
Jawabin dan takarar gwamnan jihar Sokoto, Ahmadu Sokoto
Dan takarar gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto, ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta gaza a jihar Sokoto.
A cewarsa, al'ummar jihar na cikin yunwa kuma idan ya samu nasara, zai dora daga inda tsohon gwamna Alu Wamakko ya tsaya.
Jawabin Sanata Kashim Shettima
"Idan Allah ya bamu mulki, zamu rike amana, zamu kula d aal'umma
zamu samawa dubban matasa abun yi, za'a tallafawa yan kasuwa, zamu share hawayen malaman boko da islamiyya.
Jama'a a takaice, Allah ya ce a Suratul-Rahman: Sakamakon Alheri, Alheri ne.
Mu nuna cewa yan Arewa masu amana ne, Tinubu ya yi mana hallaci.
A 2015, Kasar Yarabawa da Edo da Tinubu ke jagoranta suka bamu kuri'u miliyan 2 da muka kayar da Jonathan da su.
Lokacin sakamako ya zi, mu hada karfi da akrfe, mu cire kanmu daga kunya, a sanmu da kunya da dattaku.
Atiku ya yi shekara 8 a matsayin mataimakin shugaban kasa, ya kirga ayyuka takwas da ya yiwa Arewa. Ya kirga mutum 8 da ya gina a Arewa.
Naka, naka ne amma ba nakan da ya san aljihunsa kadai ba."
Jawabin Shugaba Majalisar dattawa, Ahmed Lawan
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya bayyana cewa APC ce ta lashe zaben gwamnan Sokoto amma akayi musus murdiya.
Lawan ya ce hujjar haka shine irin dandazon jama'ar da ke halarce a wajen taron kamfen.
Ahmad Lawan yace duk da PDP ce ke mulki a jihar Sokoto, kashi 80% na al'ummar Sokoto yan jam'iyyar APC ne.
Ya yi kira ga al'ummar Sokoto su zabi Bola Ahmed Tinubu matsayin shugaban kasa da kuma Sanata Kashim Shettima ranar 25 ga Febrairu, 2023.
A cewarsa:
"Sakkwato ta APC ce, kada mu bari ayi mana duka daya."
Jawabin shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagudu
A madadin gwamnonin jam'iyyar APC, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya bayyana cewa:
"Tun daga filin jirgin zuwa gidan Sarkin Musulumi, daga kuma fadar sarki zuwa nan, kowa ya san Sakwaato ta APC ne.
Muna kyautata zaton ranar 25 ga wata jam'iyyar APC zata lashe zabe."
Buhari, Tinubu, Shugaba APC sun dira fadar Sarkin Musulmi
Gabanin kaddamar da taron kamfen da aka shirya a filin Giginya, dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, da Shugaba Buhari sun jagoranci sauran jiga-jigan APC wajen kai gaisuwan ban girma wajen Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya karbi bakuncinsu ne inda ya musu addu'a da kuma basu shawari.
Shugaba Buhari, Tinubu, dss sun dira Sokoto
Shugaba Muhammadu Buhari ya dira cibiyar daular Usmaniyya, jihar SOkoto, domin halartan taron kamfen Asiwaju Bola Tinubu/Kashim Shettima.
Kalli bidiyon kamfen